15 Jan 2017

KA KO SAN DA WANNAN A MUSULUNCI?

HADISI NA FARKO:

MANZON ALLAH (S.A.W) ya na cewa Wanda ya karanta Qulhuwallahu Ahad kafa 10x ALLAH ya yi masa Alkawarin zai gina masa katafaren gida a gidan Aljanna. Sai Sayyidina Umar ya ce Ai to in haka ne sai mu dinga yawaitawa, sai MANZON ALLAH (S.A.W) ya ce ALLAH (S.W.T) shine mai yawaitawa ALLAH (S.W.T) shine mai tsabtacewa. 


HADISI NA BIYU :

MANZON ALLAH (S.A.W) ya na cewa duk wanda ya karanta suratul Kahfi a ranar juma'a ALLAH (S.W.T) zai cika masa hasken sa har zuwa wata juma'a mai zuwa yana cikin haske yana cikin farin ciki.

13 Oct 2016

BANBANCI TSAKANIN MANIYYI, MAZIYYI, WADIYYI, DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCEN SU

Wajibine kowani baligi ko baliga su san hukunce-hukuncen su domin gyara ibadunsu.

HUKUNCIN FITAR MANIYYI shine: fitowar sa tana wajabta wankan janaba akan namiji ko mace.

LAUNIN MANIYYIN NAMIJI: ruwane mai kauri fari wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da zakari. Sannan yana tunkudo juna lokacin dayake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari, idan ya bushe yana kamshin kwai.

LAUNIN MANIYYIN MACE: Ruwane tsinkakke, mai fatsi-fatsi, Wani lokacin kuma yana zuwa fari, wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji. Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa. Kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko damammen gari, idan ya bushe shima yana kamshin kwai.

HUKUNCINFITAR MAZIYYI: hukuncin sa shine a wanke farji gaba daya, da kuma inda ya shafa, kuma a sake alwala.

LAUNIN MAZIYYI: Ruwane tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar sha'awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce kakeso, ko matarka, ko kallon matar ko namijin da kike sha'awa. Haka kuma yana fitowa yayin wasa tsakanin miji da mata, saidai shi baya tafiyarda sha'awa, kuma wani lokacin ba'a sanin yafito.

Malamai suna cewa, Maziyyi yafi fitowa mata, fiye da maza.

HUKUNCIN WADIYYI: wadiyyi yana daukar hukunce-hukuncen fitsari ne.

WADIYYI: Wani ruwane mai kauri dayake fitowa a karshen fitsari, ko kuma karshen bahaya ga wanda ya jima bai yiba, yana fitowa ga wadanda ba suda aure, ko wadanda suka yi nisa da abokin
rayuwarsu ta aure, ina nufin namiji ko mace.

Amman fa ku sani komai saida niyya

ALLAH S.W.T shine mafi sani!!!

6 Oct 2016

MAGANIN MATSALOLI 7

Mutumin da yake cikin tsoro ya lazumci karanta: HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL.

Mutumin da bakin ciki ya dame shi ya lazumci karanta: LA ILAHA ILLA ANTA SUB'HANAKA INNEE KUNTU MINAZ ZALIMEENA.

Mutumin da masu makirci suka dame shi da makirci ya lazumci karanta: WA UFAWWIDHU AMREE ILAL LAAH. INNAL LAAHA BASEERUN BIL 'IBAADI.

Mutumin da yake fama da wata jinya ko rashin lafiya, ya yawaita karanta: RABBI ANNEE MASSANIYADH DHURRU WA ANTA ARHAMUR RAHIMEENA.

19 Apr 2016

ABUBUWA BAKWAI (7) DAKE SA MALA'IKU SUYIMA MUTUM ADDU'A.

ABUBUWA BAKWAI (7) DAKE SA MALA'IKU SUYIMA ADDU'A.


1± Lokacin da kake jiran sallah a masallaci.

2± Lokacin da kake sallah a sahun farko.

3±Fadin ameen bayan karatun fatiha.

4± Sallar subhi acikin jam'I.

5± Yin addu'a ga dan uwanka musulmi abayansa.

6± Ciyarwa fisabilillah.

20 Jan 2016

HUKUNCIN YAWAN KOKONTO A CIKIN SALLAH

mai yawan shakku shine yayi kokari wajan yin sallah cikin jama'a wato tare da liman, Idan haka bata samuba sai ya lura da kokonton Nasa dadine ko ragi Idan ragine sai yazo da abunda ya rage sai yayi sujjada ba'adi, Idan karine sai yayi sujjada ba'adassalami shima.

Kasani/kisani cewa mai mantuwa kashi Uku ne.

1- Wanda ya manta ko ya kara cikin wani Abu na farillah.

Wannan dole sai yazo da Abunda ya rage Idan yakai matsayin farillah dole sai yacikoshi sai yayi sujja bayan sallama Idan ya bai tunaba har saida ya sallame Kuma Aka samu lokaci sallar ta baci sai ya sake Idan kuma ya tuna a kusa sai ya kawo Abunda ya rage yayi sujjada bayan sallama.

19 Jan 2016

HUKUNCIN YIN JIMA'I DA AMARYA KO UWARGIDA TA DUBURA

Kamar yadda shari'a tayi hani akan aiwatar da jima'i ga uwargida ko amarya a lokacin da take haila, hakama jima'i ta dubura shari'a tayi hani mai tsanani akan aiwatar dashi.

MANZON ALLAH (S.A.W) yayi hani ga wadannan munanan aiyuka (jima'i a lokacin haila da jima'i ta dubura) a Hadisai da dama.

MANZON ALLAH  (S.A.W) yace: mutumin dake jima'i da matarsa ta dubura ALLAH Madaukakin Sarki ba zai dube shi da tausayi ba a ranar karshe.

Shehun malami Imam Ghazzali (R.A) ya rubuta a cikin littafinsa "IHYA" cewa yin jima'i da mace ta dubura yafi laifi mai tsanani akan yin jima'i da ita yayin da take haila. (A sani dukkansu laifukane masu tsanani)

LOKUTTAN DA ANSO KADA A GABATAR DA JIMA'I

Makaruhi ne ango da amarya ko maigida da uwargida su gabatar da jima'i a cikin darare ukku na kowane wata, wadannan darare kuwa sune:
1. Daren farkon kowane wata.
2. Daren karshen wata.
3. Daren tsakiyar wata.

5 Jan 2016

WANKAN JANABA (FARILLAI, SUNNONI DA MUSTAHABI) DA HUKUNCI A CIKIN WANKAN

FARILLAN WANKA: Yin niyya yayin farawa da gaggautawa da cuccudawa da gama jiki da ruwa.

SUNNONIN WANKA: Wanke hannaye ya zuwa tsintsiyar hannu kamar yadda akeyi a alwala, da kurkure baki, da shaka ruwa, da fyacewa, da wanke kofar kunnuwa itace kofa mai shiga cikin kai, amman fatar kunne wajibine a wanke cikinta da bayanta.

MU SAHABBAN WANKA: Farawa da wanke najasa, sannan a wanke azzakari inda a nan ne zaiyi niyyar wankan, sannan ya wanke gabban alwala sau dai-dai, sannan ya wanke saman jikinsa, da wanke kai sau uku da gabatar da tsagin jikinsa na dama, da karanta ruwa akan gabbai.


HUKUNCE HUKUNCEN WANKA

RANAKU DA LOKUTTAN DA ANSO A GABATAR DA JIMA'I A CIKINSU

Ranaku da aka so ango ya gabatar da jima'i  da amaryarsa, domin fa'ida da samun falalarsu.

Daren litinin, ana samun mahaddacin Alkur'ani.

Daren talata, ana samun yaro/yarinya Shahidi.

Daren alhamis, ana samu yaro/yarinya mai yawan tsoron ALLAH S.W.T, ko kuma wayayye mai kwarjini.

Ranar juma'a kafin a tafi sallar Juma'a,  ana samun yaro/yarinya mai sa'a tare da samun kyakkyawan karshe.

Jima'i a daren Juma'a na da matukar kyau domin shine mafi darajar darare guda bakwai.
Annabi S.A.W yace:

4 Jan 2016

JANABA TA KASU KASHI BIYU

na farko shine fitar maniyyi ta hanyar jin dadi na al'ada, a bacci ko a farke, ta hanyar jima'i ko waninsa.

Na biyu shine buyan hashafa (wato kan azzakari) a cikin farji.

Wanda yayi mafarki yana tarawa da mace amma maniyyi bai fito masa ba, to babu komai a kansa.

Wanda ya samu busasshen maniyyi a jikin tufansa bai san yaushe ne ya same shi ba, to yayi wanka ya sake abunda ya sallata tun daga baccin sa na qarshe da yayi da wannan tufan.