Skip to main content

Posts

Showing posts with the label FATAWA

MAGANIN MATSALOLI 7

Mutumin da yake cikin tsoro ya lazumci karanta: HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL. Mutumin da bakin ciki ya dame shi ya lazumci karanta: LA ILAHA ILLA ANTA SUB'HANAKA INNEE KUNTU MINAZ ZALIMEENA. Mutumin da masu makirci suka dame shi da makirci ya lazumci karanta: WA UFAWWIDHU AMREE ILAL LAAH. INNAL LAAHA BASEERUN BIL 'IBAADI. Mutumin da yake fama da wata jinya ko rashin lafiya, ya yawaita karanta: RABBI ANNEE MASSANIYADH DHURRU WA ANTA ARHAMUR RAHIMEENA.

HUKUNCIN YAWAN KOKONTO A CIKIN SALLAH

mai yawan shakku shine yayi kokari wajan yin sallah cikin jama'a wato tare da liman, Idan haka bata samuba sai ya lura da kokonton Nasa dadine ko ragi Idan ragine sai yazo da abunda ya rage sai yayi sujjada ba'adi, Idan karine sai yayi sujjada ba'adassalami shima. Kasani/kisani cewa mai mantuwa kashi Uku ne. 1- Wanda ya manta ko ya kara cikin wani Abu na farillah. Wannan dole sai yazo da Abunda ya rage Idan yakai matsayin farillah dole sai yacikoshi sai yayi sujja bayan sallama Idan ya bai tunaba har saida ya sallame Kuma Aka samu lokaci sallar ta baci sai ya sake Idan kuma ya tuna a kusa sai ya kawo Abunda ya rage yayi sujjada bayan sallama.

YADDA AKEYIN SALLAR GAWA

Yanda Akeyin Sallar gawa daga Annabi (saw). Kamar yanda wasu daga cikin 'yan uwa  Suka nema cewa Ayiwa mutane Karin bayani Akan Sallar Jana'iza Muna Rokon Allah ya bamu dacewa cikin Abunda zamu fada. Da farko dai mutum Zai Qudurta Niyya a ransa. Idan Namiji ne mamacin Sai liman ya tsaya saitin kan sa, Idan Mace ce Sai liman ya tsaya tsakiyar ta daidai. Sai yayi kabbara ta farko, sai Fathi daya da sura cikin gajerun Surori ko wasu Ayoyi a takaice Sai ya sake Kabbara ta biyu, sai ya kawo Salati ga Annabi (saw) Salatu Ibrahimiyya. Sai yayi kabbara ta Uku, bayan kabbara ta Uku sai ya kawo wannan Adu'ar

MAGANIN KARFIN MAZA KO MATA A MUSULUNCE

kala-kalar abincin dake samar da karfin maza/mata  (sperm), da kuma kuzari a jikin ango da amarya. HATSI: 1. Alkama ko kuma duk wani dangin abinci da ake samarwa daga gareta. 2. Shinkafa. 3. Wake. GANYE: 1. Albasa. 2. Galik. 3. Karas. 4. Dankali. 5. Kwakwa. 'YA' YAN ITATUWA: 1. Ayaba. 2. Mangoro.

ISTIMNA'I (masturbation) da HUKUNCIN SA

ISTIMNA'I ( masturbation) shine shine mutum ya rika wasa da al'aurassa har ya fitar da maniyyi, HUKUNCIN ISTIMNA'I Farko dai akwai hadisai wadanda suka nuna fushi na ubangiji akan mai aikata hakan, Hukuncinsa ga malaman mazhabobi guda hudu, Imam Malik Imam Shafi'i. Sun tafi akan haramta shi don haka a wurin su dole mutum yayi aure ko ya kame har zuwa lokacin da Allah zai bashi ikon yin aure.

ADDUAR DA MANZON ALLAH (SAWW) YAKE KARANTAWA IDAN ZAI KWANTA BARCI

ﺑِﺎﺳْﻤِﻚَ ﺭَﺑِّﻲ ﻭَﺿَﻌْﺖُ ﺟَﻨْﺒِﻲ، ﻭَﺑِﻚَ ﺃَﺭْﻓَﻌُﻪُ، ﻓَﺈِﻥْ ﺃَﻣْﺴَﻜْﺖَ ﻧَﻔْﺴِﻲ ﻓَﺎﺭْﺣَﻤْﻬَﺎ، ﻭَﺇِﻥْ ﺃَﺭْﺳَﻠْﺘَﻬَﺎ ﻓَﺎﺣْﻔَﻈْﻬَﺎ، ﺑِﻤَﺎ ﺗَﺤْﻔَﻆُ ﺑِﻪِ ﻋِﺒَﺎﺩَﻙَ ﺍﻟﺼَّﺎﻟِﺤِﻴﻦَ . Bismika Rabbee wadha'atu janbee , wa bika 'arfa'uhu, fa'in 'amsakta nafsee farhamhaa, wa 'in 'arsaltahaa fahfaz'haa, bimaa tahfazu bihi 'ibaadakas-saal iheen.

ISTIGFARIN DAYA FI KOWANE ISTIGFARI

Allahumma anta rabbi lailahailla anta kalaqtani, wa ana abduka wa ana ala ahadika wawa'adika mastada'atu auzubika min sharri maa sana'atu, abu'ulaka bi ni'imatika alaiya wa abu'ubizambi fagfirli fa innahu layagafiru zunuba illa anta. wanda duk ya fadeta da rana yana mai yakini da ita sai ya mutu a wannan yinin wannan yana daga ahlin aljanna. wanda ya karanta da dare shima da yakini akanta shima dan aljanna ne. Salati 10 ga Annabi S.A.W 

SALATUL ISTIHARA

MANZON ALLAH mai tsira da amincin ALLAH ya kasance yana sanar damu yanda ake istihara acikin kowane irin al'amurra da muka kasance, harma yake cewa 'duk lokacin da daya daga cikinku ya kasance mai himmatuwa ya zuwa wani aiki to sai yai sallah raka'a biyu (2) sannan sai yace  "ALLAHUMMA INNI ASTAKIRUKA BI ILMIKA WA'ASTAQADIRUKA BI QUDIRATIKA WA'AS'ALUKA MIN FADALUKAL AZIM FA INNAKA TAQDIRU WALA AQDIRU Fa AnTA taALAMU WALA A'ALAMU WA'ANTA ALLAMULGUYUB, ALLAHUMMA IN KUNTA TA'ALAMU ANNA HAZAL AMRA KHAIRUNLI FIDINI WA MA'ASHII WA'AQIBATU AMRI"  Ko kuma mutum yace

FAIDODIN SALATUN NABIYYI (SAWW)

Idan ka yawaita salati da tasleemi ga Manzon Allah (saww) zaka samu rabauta da fa'idodi Masu yawa Kamar haka: 1. Cika Umurnin Allah da yace: "Salluu 'alaihi wa sallimuu tasleeman". 2. Allah zai maka salatai guda 10 IRIN NASA (SWT). 3. Allah zai sa Mala'ikinsa ma suyi maka salati. 4. Zaka samu biyan bukatarka da gaggawa, domin kuwa Salatun Nabiyyi (saww) shine mabudin kofar samun karbuwar Addu'a.

Dr Maqary yakan ce

"Yanzu alumman musulmi sun zama in dai suna son mutum  ko don kungiyansu daya ko aqeeda ko Wani dalili dai ya hada su tohm baya laifi a  wurrinsu duk ko girman laifin da yayi Zaa nemi uzuri... Idan yana iskanci ace  jazba ne. Idan asharari ne ace sahibul haal ne... Idan kuwa baa son shi tohm Abu  kadan Zai fada ko da ba hakan ya nufa ba a juya mashi magana ayi tawili ace ai  Ga abunda yake nufi ... Kuma ayi ta yayatawa..." Rab Sitteer ya rajul

CETON ANNABI GASKIYA NE

Shine farkon wanda zai nemi ceto awajen Ubangijinsa, kuma shine farkon wanda  za'a bama damar yayi ceto 1. Da farko zai ceci dukkan halitta, albarkacin ceton nasa (S.A.W.W) ne ma Ubangiji zai saurari halitta harma ayi musu hisabi 2. Akarkashin cetonsa (S.A.W.W) ne Sauran Annabawa da Manzanni suma zasuyi ceto abisa al'ummominsu 3. Waliyyan Allah, Shahidai da sauran Muminai su ma zasuyi ceto akarkashin cetonsa (S.A.W.W) 4. Zai ceci Ma'abota tarin Zunubi daga cikin al'ummarsa (S.A.W.W), Sanna daga Qarshe zaije har cikin Jahannama ya rika fidda Mutane. Ba zai bar duk wani Musulmi ko Mumini ba, sai ya fidda dukkan wanda yake da Imani azuciyarsa koda Misalin Kwayar Zarrah ne Ya Allah Domin falalarka da Rahamarka, Don Girman Jamalar Zatinka ka sanyamu acikin wadanda zasu shiga Aljannah ba tare da hisabi ko Uqubah ba.

TAFARKIN TSIRA

ANNABI (SAW) yana cewa: Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Yaa Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani. Kasa mucika da imani.

LADUBBAN SALLAMA

1. Mustahabi ne idan anyi sallama a hada hannu. Annabi(saw) yace wanda suka hada hannu za'a gafar ta musu zunuban su. 2. Kuma anfi so mutum ya fara gaisawa da mutane daga hannun daman sa. 3. Bayan mutum zai bar cikin mutane zai sake yin sallama. Manzon Allah (saw) yace tafarkon ba tafi ta karshen ba, ma'ana ladan su iri dayane. 4. Wanda yake tafiya shi zai yiwa na zaune, wanda yake kan abin hawa yayi wa mai tafiya. Wanda ya fara yin sallama lokacin da aka hadu shi yafi samun falala. 5. Ko kasan mutum ko bakan sanshi ba za kayi masa sallama. 6. Namiji zai iya yiwa mace, mace ma zata iya yiwa namiji sai de a kyautata niya. 7. Amma masu cewa Salamu'alaikum wannan ba sallama bace hausane kawai, amma yazo acikin Alqur'ani za ka iya cewa Salamun'alaikum. Hukunce-hukuncesallama yana da yawa mutum ya duba AL-ADABUL MUFRAD na Imamul Bukhari don karin bayani Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W 

NIYYAR YANKAN LAYYAH DAGAGIDAN ANNABI (SAW)

ﻣﻦ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻟﻤﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﺃﻥ ﻳﺬﺑﺢ ﺍﻷﺿﺤﻴﺔ yanadaga sunnar ma'aiki gawanda yake da niyyar yanka layyarsa, ﺃﻥ ﻳﻘﻮﻝﻋﻨﺪ ﺍﻟﺬﺑﺢ yafadi wannan kalmar lokacin da zaiyi yanka. ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻫﺬﺍ ﻣﻨﻚ ﻭﻟﻚ ، ﻫﺬﺍ ﻋﻨﻲ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺗﻘﺒﻞ ﻣﻨﻲ ) IDAN KUMA WANI ZAKA YANKAWA SAI KACE