Skip to main content

Posts

Showing posts with the label HUKUNCI

HUKUNCIN HAYAR MAHAIFA, DA SAYAR, KO KYAUTAR DA KWAYOYIN HALITTA A MUSULUNCI KASHI NA UKU

HUKUNCIN HAYAR MAHAIFA, DA SAYAR, KO KYAUTAR DA KWAYOYIN HALITTA A MUSULUNCI KASHI NA UKU 2 - Hukuncin idan matar da aka ari mahaifarta ta zamo kishiyar mai kwayoyin halitta: Mun bayyana cewa malaman Shari’ar Musulunci sun hadu akan haramci bayar da hayar mahaifa, idan mai mahaifar ba ta da dangantaka ta aure da namijin da aka hada maniyyin sa da kwayoyin halittar da aka ciro daga maniyyin matarsa.. Haka ma haramun ne a hada maniyyin namiji da kwayoyin halittar wata macen da ba matarsa ba; domin a shigar a cikin mahaifar matarsa.. Amma idan matar da za ta bayar da mahaifar tata kishiya ce ta mai kwayoyin halittar, ma’ana: matan mutum daya ne, mijinsu daya, to a nan malamai sun yi sabani; wasu suna ganin babu laifi a yi hakan saboda lalura, ganin cewa dukansu matan mutum daya ne. Wasu malaman kuma suna ganin cewa hakan haramun ne, domin ba shi da wani bambanci da surar farko da muka bayyana.. “al-Majma’ul Fiqhiy al-Islamiy”: wato Kungiyar masana ilimin F...

HUKUNCIN HAYAR MAHAIFA, DA SAYAR, KO KYAUTAR DA KWAYOYIN HALITTA A MUSULUNCI KASHI NA BIYU

HUKUNCIN HAYAR MAHAIFA, DA SAYAR, KO KYAUTAR DA KWAYOYIN HALITTA A MUSULUNCI KASHI NA BIYU HUKUNCIN HAYAR MAHAIFA” DA “SAYAR KO KYAUTAR DA MANIYYI KO KWAYOYIN HALITTA” Mun bayyana irin yanda wannan aiki na bayar da hayar mahaifa yake, da kuma yanda yanda ake sayar, ko kyautar da maniyyi, ko kwayoyin halitta a rubutun da ya gabata, inda muka bayyana surorinsu guda hudu, a yanzu -cikin ikon Allah- za mu hade wadanda suka yi kama da juna mu ambaci hukuncinsu kaman yanda malaman Shari’ar Musulunci suka bayyana.

HUKUNCIN HAYAR MAHAIFA, DA SAYAR DA KO KYAUTAR DA KWAYOYIN HALITTA (MANIYYI) A MUSULUNCI KASHI NA DAYA

HUKUNCIN HAYAR MAHAIFA, DA SAYAR, KO KYAUTAR DA KWAYOYIN HALITTA A MUSULUNCI KASHI NA DAYA SHIMFIDA: Cigaban da aka samu –mai yawa- a fannin ilimin kimiyya da fasaha ya yi sanadiyyar sauyawan abubuwa masu yawa da aka sani a da, kaman yanda ya furzar da abubuwan da babu wanda ya taba tunanin cewa za su iya faruwa, wannan abu kuwa ya shafi fannonin: zamantakewa, da ilimin sadarwa, da kuma ilimin likitanci. A shekarun baya-bayan nan ne ilimin likitanci ya kawo wani gagarumin sauye - sauye a bangaren haihuwa, inda –a karon farko- duniya ta fara jin kalmomi irin su: “Hayar mahaifa” da “Bankin sayar da maniyyi” da “mahaifar kwalba” da “Istinsakh” (wato samar da jariri ba ta hanyar miniyyin namiji da mace ba) ko “colony” a Turance, da sauransu. Duk da cewa asalin wadannan abubuwa sun faru ne a kasashen da ba na Musulmi ba, sai dai cikin gaggawa suka tsallaka zuwa kasashen Musulmai, wasu kuma Musulman suka fara tsallakawa zuwa kasashen da ake yin wadannan ayyuka a asibitocinsu domin...

HALACCIN YIN GWAJI (AWO) KAFIN AURE

Babu laifi a yi gwajin Genotype, ya ma inganta Manzon Allah SAW Ya yi umurni da abu makamancin haka, sannan idan ya bayyana akwai qaqqarfar yuyuwar haihuwan yara SS babu laifi a fasa wannan auren. ALLAH SWT Ne masani Amsa daga Dr Ibrahim Maqary Zaria

HUKUNCIN SIYAN KAYAN DA HUKUMAR CUSTOM TAYI GWANJO

Hukumar Custom tana yin gwanjo ne na kayan da ta kwace a hannun wadanda suka karya dokokin shiga da ficen kayayyaki kaman yarda doka ta tanadar Shi dai shige da fice na kayan da gwamnati ta hana ta barauniyar hanya yana cutar da tattalin arzikin kasa. Shi kuma cutar da tattalin arzikin kasa cutar da al'umma ne baki daya wanda kuma haram ne ka cutar da yan'uwanka.

HUKUNCIN YAWAN KOKONTO A CIKIN SALLAH

mai yawan shakku shine yayi kokari wajan yin sallah cikin jama'a wato tare da liman, Idan haka bata samuba sai ya lura da kokonton Nasa dadine ko ragi Idan ragine sai yazo da abunda ya rage sai yayi sujjada ba'adi, Idan karine sai yayi sujjada ba'adassalami shima. Kasani/kisani cewa mai mantuwa kashi Uku ne. 1- Wanda ya manta ko ya kara cikin wani Abu na farillah. Wannan dole sai yazo da Abunda ya rage Idan yakai matsayin farillah dole sai yacikoshi sai yayi sujja bayan sallama Idan ya bai tunaba har saida ya sallame Kuma Aka samu lokaci sallar ta baci sai ya sake Idan kuma ya tuna a kusa sai ya kawo Abunda ya rage yayi sujjada bayan sallama.

HUKUNCIN YIN JIMA'I DA AMARYA KO UWARGIDA TA DUBURA

Kamar yadda shari'a tayi hani akan aiwatar da jima'i ga uwargida ko amarya a lokacin da take haila, hakama jima'i ta dubura shari'a tayi hani mai tsanani akan aiwatar dashi. MANZON ALLAH (S.A.W) yayi hani ga wadannan munanan aiyuka (jima'i a lokacin haila da jima'i ta dubura) a Hadisai da dama. MANZON ALLAH  (S.A.W) yace: mutumin dake jima'i da matarsa ta dubura ALLAH Madaukakin Sarki ba zai dube shi da tausayi ba a ranar karshe. Shehun malami Imam Ghazzali (R.A) ya rubuta a cikin littafinsa "IHYA" cewa yin jima'i da mace ta dubura yafi laifi mai tsanani akan yin jima'i da ita yayin da take haila. (A sani dukkansu laifukane masu tsanani)

ABUBUWAN DAKE WARWARE ALWALA

Abubuwan da suke warware alwala sune kari da sabanin kari. Kari shine: fitsari da gyangyadi da rihi da maziyyi da wadiyyi. Sabanin kari sune: bacci mai nauyi da suma da maye da hauka da sumbata da shafar mace idan anyi niyyar jin dadi ko an samu jin dadin da shafar azzakari da cin tafin hannu ko cin yatsu. Hukuncin kari. Wanda yayi kokwanto a cikin kari ya wajaba a kansa ya sake alwala, sai dai idan ya kasance mai yawan kokwanto ne to babu komai a kansa. Ya wajaba a kansa ya wanke azzakarinsa gaba daya idan mazziyi ya fito, amman bazai wanke maraina ba. Note: mazziyi ruwa ne mai fitowa yayin karamar sha'awa ta hanyar tunani ko kallo ko waninsa. Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W 

ISTIMNA'I (masturbation) da HUKUNCIN SA

ISTIMNA'I ( masturbation) shine shine mutum ya rika wasa da al'aurassa har ya fitar da maniyyi, HUKUNCIN ISTIMNA'I Farko dai akwai hadisai wadanda suka nuna fushi na ubangiji akan mai aikata hakan, Hukuncinsa ga malaman mazhabobi guda hudu, Imam Malik Imam Shafi'i. Sun tafi akan haramta shi don haka a wurin su dole mutum yayi aure ko ya kame har zuwa lokacin da Allah zai bashi ikon yin aure.