Abubuwan da suke warware alwala sune kari da sabanin kari.
Kari shine: fitsari da gyangyadi da rihi da maziyyi da wadiyyi.
Sabanin kari sune: bacci mai nauyi da suma da maye da hauka da sumbata da shafar mace idan anyi niyyar jin dadi ko an samu jin dadin da shafar azzakari da cin tafin hannu ko cin yatsu.
Hukuncin kari.
Wanda yayi kokwanto a cikin kari ya wajaba a kansa ya sake alwala, sai dai idan ya kasance mai yawan kokwanto ne to babu komai a kansa.
Ya wajaba a kansa ya wanke azzakarinsa gaba daya idan mazziyi ya fito, amman bazai wanke maraina ba.
Note: mazziyi ruwa ne mai fitowa yayin karamar sha'awa ta hanyar tunani ko kallo ko waninsa.
Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W
Shin shafan zakari da hanu ba da nufin jin dadi ba yana warware alawala?
ReplyDeleteS.A.W.
ReplyDelete