Farilla
alwala: niyya da wanke fuska da wanke hannaye zuwa gwiwar hannu da shafar kai
da wanke kafafuwa zuwa ido-sawu da cucudawa da gaggautawa.
Sunnonin
alwala: wanke hannaye izuwa tsintsiyar hannu yayin farawa, da kurkure baki, da
shaka ruwa, da fyacewa, da dawo da shafar kai, da shafar kunnuwa, da sabunta
ruwa dan shafar kunnuwa, da jeranta farillai.
Mustahabban
alwala: yin bisimilla, da yin asuwaki da karawa a bisa wankewa ta daya a fuska
da hannaye da fara shafar kai daga goshi da jeranta sunnoni da karanta ruwa a
kan gabbai da gabatar da wanke dama a kan hagu.
Ya wajaba a tsefe yatsun hannaye, an
so tsefe gashin gemu mara duhu a cikin alwala amma ban da mai duhu. Ya wajaba a
tsefe shi a cikin wanka ko da mai duhu ne.
Gyaran
alwala:
Wanda
ya manta farilla daga gabbansa na farilla, idan ya tuna a kusa sai ya wanke
wannan farillar kuma ya sake wanke abinda yake bayanta, idan kuwa lokaci ya yi
tsawo sai ya wanke ta ita kada ya sake sallar da ya yi kafin ya wanke din.
Idan
kuma ya bar sunna sai ya wanke ta ba zai sake salla ba. Wanda ya manta gurbin
da bai sami ruwa sai ya wanke shi, shi
kadai ba tare da niyya ba. Idan ya riga ya yi salla kafin wannnan sai ya sake.
Wanda
ya tuna kurkure baki ko shaka ruwa bayan ya fara wanke fuska, ba zai dawo zuwa
gare su ba har sai ya gama alwalarsa.
::ALLAH
NE KADAI MASANI.