Skip to main content

Posts

Showing posts with the label TARIHI

Sayyiduna Abubakrin R.A

Sayyiduna Abubakrin bai fifici sauran Sahabbai da yawan Sallah ko yawan Azumi, ko yawan Ruwayar Hadisai ba. Sai dai ya Fificesu ne da Yawan Soyayyar Manzon Allah (S.A.W.W). Wannan Soyayyar ta sanya ba ya ganin komai agabansa sai Allah da Manzonsa (S.A.W.W). Kuma wannan Soyayyar ce ta sanyashi yake da saurin Gaskatawa da zarar wani Umurni ko hani ya sauka. Wannan Soyayyar ce ta sanya Allah ya zabeshi ya zama Khalifan farko daga cikin Khalifofin Masoyinsa (S.A.W.W). Haka nan shima Manzon Allah (S.A.W.W) yana mutukar Qaunar Sayyiduna Abubakar (R.A). Har Watarana Sayyiduna Amru bn Al-aas (R.A) ya tambayi Manzon Allah (S.A.W.W) Wanene Wanda kafiso acikin Mutane baki dayansu?" Sai yace masa "A'isha". Sai yace "Acikin Maza fa?" Sai yace "Abubakar ne". Mutane sukan fuskanci bacin rai sosai daga Manzon Allah (S.A.W.W) aduk lokacin da suka 'bata ran Sayyiduna Abubakrin. Wannan Qarfin Soyayyar ce ta sanya Sayyiduna Abubakrin yafi kowa Imani...

Sayyiduna Uthman bn Affaan (ra) yace

Mutumin da yasan Allah, sani NA HAQIQA, yana da wasu alamomi guda takwas (wadanda ake ganeshi dasu). 1 & 2. Zuciyarsa zata kasance cike da tsoron Azabar Allah, da kuma kwadayin rahamarsa. 3&4. Harshensa zai kasance ko yaushe cikin furta yabo ga Allah, da kuma bayyana gidiyarsa gareshi. 5&6. Idanuwansa zasu kasance ko yaushe cikin Jin kunyar Ubangijinsa, da kuma Zubda hawaye cikin tunaninsa. 7&8. Zai kasance cikin Burin rabuwa da duniya ako yaushe, da kuma neman yardar Ubangijinsa. Ya Allah ka azurtamu da wadannan Halayen. Fatiha da salati 10 ga SHUGABA S.A.W. 

DARAJOJI GUDA 10 GAME DA SAYYIDUNA UTHMAN BN AFFAN (rta)

DARAJOJI GUDA 10 GAME DA SAYYIDUNA UTHMAN BN AFFAN (rta) Kafin mutuwar Shahadarsa, Sayyiduna Uthman (ra) ya gaya ma ABU THAWR AL- FAHMIY cewa: "Ina Kyautata zato awajen Ubangijina saboda wasu abubuwa guda goma wadanda na sanyasu amatsayin amana tsakanina dashi. Abubuwan sune: 1. Nine mutum na hudu wajen shiga Musulunci. 2. Manzon Allah (saww) ya aura min 'Yarsa ta cikinsa. 3. Da ta mutu ya Qara aura min da 'Yar uwarta. 4. Tunda nake ban ta'ba rera waka ba. 5. Tunda nake ban ta'ba Tunanin aikata mugunta ba. 6. Tun daga ranar da nayi mubaya'a ga Manzon Allah (saww) da hannuna na dama, ban sake shafar al'aurata da wannan hannun ba.

KADAN DAGA YADDA BILAL YAKE SON SHUGABA S.A.W

WANI LAMARI MAI GIRGIZA ZUCCIYAR MASOYAN ANNABI MUHAMMADU S.A.W YA FARU BAYAN WAFATINSA yayinda sayyiduna Bilal yaga damuwa da kadaicin rabuwa da babban masoyinmu ya tsananta gareshi madina ta zamemashi tamkar keji abu ya zamo ko kiransallah baya iyayi domin da ya kawo wurin "ASH HADU ANNA MUHAMMADURRASULULLAH" sai yaji muryarsa ta shake ta tsaya don kuka da kaunar annabi S.A.W gani yake kamar zai waiwaya yagansa . Da yaga abu yatsananta gareshi saiya nemi iznin khalifa sayyiduna Abubakar Assaddiq R.A don ya tashi ya koma kasar Sham ya zauna acan tareda wasu cikin sahabban manzon Allah.