WANI LAMARI MAI GIRGIZA ZUCCIYAR MASOYAN ANNABI MUHAMMADU S.A.W YA
FARU BAYAN WAFATINSA
yayinda sayyiduna Bilal yaga damuwa da kadaicin rabuwa da babban masoyinmu ya tsananta gareshi madina ta zamemashi tamkar keji abu ya zamo ko kiransallah
baya iyayi domin da ya kawo wurin "ASH HADU ANNA MUHAMMADURRASULULLAH" sai
yaji muryarsa ta shake ta tsaya don kuka da kaunar annabi S.A.W gani yake kamar zai waiwaya yagansa .

Da yaga abu yatsananta gareshi saiya nemi iznin khalifa sayyiduna Abubakar Assaddiq R.A don ya tashi ya koma kasar Sham ya zauna acan tareda wasu cikin
sahabban manzon Allah.
sahabban manzon Allah.
Ya nacan zaune tsawon lokaci sai rannan kwatsam yayi mafarki da shugaban halittun Allah Annabi Muhammadu S.A.W yana ce masa :
YAKAI BILAL WANNAN WACE IRIN KEKASHEWACE ? HAR YANZU LOKACI BAI ZOBA DA
ZAKAZO KA ZIYARCEMUBA ?
Ko da sayyiduna Bilal ya farka bai jira komaiba ya hau doki a guje bai zame koinaba sai Madina yana zuwa yazarce dausayin aljanna a duniya Rauda ma daukakiya makwantar annabin farko da karshe annabin rahama S.A.W ya isa gaban fiyayyen kabari yana kuka yana birgima yana dibar kasa yana zuba ma kansa .
Ana cikin haka jikokin annabin tsira sadatuna Hassan da Hussaini R.A suka tarar dashi suka rinka goge masa kasa suma suna kuka suna rungume dashi.
Daganan aka nemi alfarmar yayi kiran sallah, baiyi gardamaba ya hau mumbari ya fara kira saiga masallaci ya cika da jamaa daga ko ina ana kyarma ana tunanin Annabi Muhammadu s.a.w dai dai lokacin da ya ambaci
"ASH HADU ANNA MUHAMMADURRASULULLAH "
Gaba daya kowa dake wurin saida ya barke da kukan tunawa da annabi Muhammadu S.A.W .
ALLAH KABAMU ALBARKACIN MASOYAN ANNABI MUHAMMADU S.A.W DUK INDA SUKE
KA AZURTAMU DA WANNAN SOYAYYA A ZAHIRI DA BADININMU
Salati 10 ga Annabi S.A.W
Comments
Post a Comment