Shine farkon wanda zai nemi ceto awajen Ubangijinsa, kuma shine farkon wanda za'a bama damar yayi ceto
1. Da farko zai ceci dukkan halitta, albarkacin ceton nasa (S.A.W.W) ne ma Ubangiji zai saurari halitta harma ayi musu hisabi
2. Akarkashin cetonsa (S.A.W.W) ne Sauran Annabawa da Manzanni suma zasuyi ceto abisa al'ummominsu
3. Waliyyan Allah, Shahidai da sauran Muminai su ma zasuyi ceto akarkashin cetonsa (S.A.W.W)
4. Zai ceci Ma'abota tarin Zunubi daga cikin al'ummarsa (S.A.W.W), Sanna daga Qarshe zaije har cikin Jahannama ya rika fidda Mutane. Ba zai bar duk wani Musulmi ko Mumini ba, sai ya fidda dukkan wanda yake da Imani azuciyarsa koda Misalin Kwayar Zarrah ne
Ya Allah Domin falalarka da Rahamarka, Don Girman Jamalar Zatinka ka sanyamu
acikin wadanda zasu shiga Aljannah ba tare da hisabi ko Uqubah ba.
acikin wadanda zasu shiga Aljannah ba tare da hisabi ko Uqubah ba.
Nice
ReplyDelete