1. Mustahabi ne idan anyi sallama a hada hannu. Annabi(saw) yace wanda suka hada hannu za'a gafar ta musu zunuban su.
2. Kuma anfi so mutum ya fara gaisawa da mutane daga hannun daman sa.
3. Bayan mutum zai bar cikin mutane zai sake yin sallama. Manzon Allah (saw) yace tafarkon ba tafi ta karshen ba, ma'ana ladan su iri dayane.
4. Wanda yake tafiya shi zai yiwa na zaune, wanda yake kan abin hawa yayi wa mai tafiya. Wanda ya fara yin sallama lokacin da aka hadu shi yafi samun falala.
5. Ko kasan mutum ko bakan sanshi ba za kayi masa sallama.
6. Namiji zai iya yiwa mace, mace ma zata iya yiwa namiji sai de a kyautata niya.
7. Amma masu cewa Salamu'alaikum wannan ba sallama bace hausane kawai, amma yazo acikin Alqur'ani za ka iya cewa Salamun'alaikum. Hukunce-hukuncesallama yana da yawa mutum ya duba AL-ADABUL MUFRAD na Imamul Bukhari don karin bayani
Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W
Comments
Post a Comment