Hadisi na farko daga littafi mai albarka na imamu Muhyiddin abu zakariyya, yahya dan sharafu annawawy Allah yai rahma agareshi madawwamiya.
Ana kiran wannan littafi da Arba'inannawawy, saboda dan ganta sunan zuwa ga wanda yarubutashi(shine imamu annawawy) kuma nasabarsa(nawawy).
Sannan malam Ahmad dan Abdurrahman dan rajab ya qara Hadisi takwas(8) daga cikin wannan littafi saboda haka suka zama hadisai hamsin kenan.
Malamai dayawa sunyi sharhin wannan littafi, a cikinsu akwai sharhin Ahmad dan Abdurrahman dan Rajab a cikin littafinsa mabayyani mai suna(Jami'ul Uluumi Wal Hikami).
Daga qarshe muna rokon Allah ya bamu ikon yin wannan aiki mai girma da muka dauko.
(HADISI NA FARKO)
An karbo wannan hadisi daga sarkin muminai, baban Hafsin Umar dan Kaddabi Allah ya qara yarda agareshi ameen.
Yace! naji MANZON ALLAH(S.A.W) yana cewa: Lallai dukkan ayyuka basu tabbata saida niyya, kuma yana ga dukkan kowane mutum abunda yai niyya, wanda hijirarsa ta zama zuwa ga ALLAH da MANZONSA ne, hijirarsa tana ga ALLAH da MANZONSA, wanda kuma hijirarsa tazama yayi tane dan duniya, to zai sameta, koko wanda yai hijirarsa dan macene to zai aureta, Hijirarsa tana ga abunda yai jihira gareshi.
Shugaban masu Hadisaine ya ruwaitoshi, Shine(Abu Abdullahi) baban Abdullahi Muhammadu dan Isma'ila dan Ibrahima dan Mugeerah dan bardiziba(Albukhariyyu) mutanen garin bukara kenan.
Yaruwaito wannan Hadisi a littafinsa mai albarka(Sahihul Bukhari) juz'i na daya (1) a hadisi na farko.
Sannan(Abul husaini) baban Husaini Musilim dan Hajjaj dan Muslim bakushaire dan garin naisabura, a Hadisi na (7091).
A cikin ingantattun litattafansu, wadanda sune mafi ingancin littattafan hadisi. Allah yasa mu dace

Comments
Post a Comment