TSARKI
YA KASU KASHI BIYU: Tsarkin kari da tsarkin dauda, gaba dayansu ba sa inganta
sai da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa, shine wanda launinsa bai jirkita ba da
basa haduwa da shi a bisa hali mafi yawa, kamar misalin narkakken mai da
sandararren mai da romo gaba dayansu da shuni da sabulu da dauda da
makamancinsu, babu laifi idan ya hadu da tulbaya da kasar kanwa da kasar
gishiri da jar kasa da makamancinsu.
FASALI:
idan najasa ta ayyana (wato aka san wurin da take) sai a wanke wurinta, idan ta
rikitar sai a wanke tufan gaba dayansa
samuwar najasa sai ya yayyafa ruwa, idan
wani abu ya same shi ya yi kokwanto a cikin najasarsa to babu yayyafi a kansa.
Wanda ya tuna najasa yana cikin salla sai ya yanke sai dai in ya ji tsoron fitar
lokaci, wanda ya yi salla da najasa yana mai mantawa, sai ya tuna bayan sallama
to ya sake salla a cikin lokaci.
::ALLAH NE MASANI