Kashi na 1
Allah kayi tsira da Aminci a bisa ainihin rahamar Ubangiji, kuma wanda yake shine (ya'aqut) na gaskiya Shi ya'aqut wani ma'adanine wanda yafi dukkan ma'adanai tsada don haka aka kamantashi da manzon Allah don manzon Allah shine yafi komai tsada Duniya da Lahira Wannan tsadar itace ta zamanto matattarar dukkan ilimomi na zahiri da badini Kuma shine hasken duk wani abin halitta wanda yake daga Annabi Adam Kuma ma'abocin gaskiya wanda yake gaban dukkan kowa a fadar ubangiji Haske wanda ya hudo ko ya fito da ma'aunoni na ribobi wadanda suke cike da rahamomi ga dukkan zukatan da suke cike da zikiri na waliyan Allah da bayi salihai Kuma haskene wanda dashine Allah ya haskakawa bayinsa suka gane hanya madaidaiciya dashi wanda yake tattare da dukkan girma na matsayi.

Kashi na 2
Allah kayi tsira da Aminci a bisa wanda yake shine ainifin hakikanin gaskiya wadda ainifin ni'imomin ubangiji da tabbatuwar ubangiji suke bayyana daga ita wannan gasikiyar wato manzon Allah kenan Wanda shine ainifin dukkan sannai idan Allah ya sanar dakai matsayin manzon Allah kamar ya sanar da kai dukkan komai Kuma shine mafi tsayuwa akan gaskiya domin gina gaskiya Sannan shine tafarkin ubangiji wanda yake cikakken tafarki na tsira kuma mafi daidaituwan dukkanin wani tafarki ko (hanya)
Kashi na 3
Allah kayi tsira da Aminci a bisa gaskiyar data bayyanar da gaskiya, wadda take taska ce mafi girman taskoki, Manzon Allah Alheri ne mai yawa wanda Alheri ya fito daga gareshi kuma zai koma gareshi, Kuma kewayayye shi manzon Allah kuma abun nema.
Kashi na 4
Allah kayi salati gareshi da kuma Ahlin gidansa salati wanda dalilin salatin zaka sanar damu ko waye Manzon Allah (saw), Wannan a dunkule kenan don gaskiya akwai wuraren dake bukatar magana fiye da wadda nayi anan. Allah yasa mu dace amin.
Daga- Malam Jamilu Abdullahi Dutsin-ma
Salati 10 ga Annabi S.A.W