Yin
nadama akan abinda ya wuce, da yin niyyar ba za a sake komawa kan sabon ba har
abada. Kuma ya bar sabon nan-take idan ya kasance yana cikin aikin sabon ne.
bai halatta a gare shi ba ya jinkirta tuba, bai halatta ba ya ce; in ALLAH ya shirye
ni na tuba ba, fadar haka yana daga alamomin rashin arzikin lahira da tabewa da
rashin basira.
1. Nafarko su fara da gaisuwa irin wadda addinin muslunci ya tanadar mana (watau suyi wa junan su sallama). 2. Sai ango ya daura hannunsa a bisa goshin amaryarsa ya karanta wannan addu'ar: "Allahumma innee as'aluka min khairiha wa khairi maa jabaltaha 'alaihi wa'a uzhubika min sharriha wa sharri maa jabaltaha 'alaihi" ( Abu Dawud Ibn Maajah Al-Haakim Al-Bahaki da Abu ya'ala). 3. Daga nan sai ango da amarya su gabatar da Alwala sannan su gabatar da Sallah raka'a biyu bayan sun idar sai su karanta addu'o'i na neman 'ya'ya na gari.