Skip to main content

KHUDUBAR ANNABI MUHAMMAD(S.A.W) TA RANAR TARA GA WATAN ZUL-HIJJAH

KHUDUBAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM WANDA YAYI A KHUDUBAR RANAR TARA GA WATAN ZUL-HIJJAH, SHEKARA TA GOMA DA HIJIRA A DUTSEN ARAFAT (RANAR ARFA KENAN).
ANNABI (SAW)YA FARA DACEWA: “Ya ku mutane ku bani hankalinku, domin mai
Yiwuwa bazan sake kasancewa da ku bayan wannan shekaran ba, saboda haka ku
saurari abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar da abinda zan gaya maku) ga wadanda basa wannan wuri a yau.
Ya ku mutane kamar yadda kuka riki wannan wata, (na hajji) da wannan rana (ta arfa) da kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma abin tsarewa, to, haka kuma ku riki Ran Musulmi da kuma Dukiyoyinsu da girma abin kuma karewa,
ku maida wa Mutane kayan da suka baku Amana. Kar ku cuci kowa, saboda kar
wasu su cuce ku, ku tuna fa, hakika ALLAH zai yi sakayya akan ayukakanku, ALLAH (SWT) ya hana cin riba,(wato kudin ruwa) saboda haka, duk abin da aka kulla
ta kudin ruwa sai a warware shi.
Ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye Addininku. Yanzu kan ya fidda ran batar da ku akan manyan abubuwa (na sabo) saboda haka ku guji binshi akan kanana.
Ya ku jamaa hakika kuna da hakki bisa matayenku, amma suma suna da hakki
bisa kanku, to hakkin su ne akanku da kuciyar dasu, Kuma ku tufatar dasu akan jin kai. ku bi dasu kyakkyawan biyarwa, ku kuma tausasa musu domin su majibintan al amurrankune,kuma mataimakan ku, Hakki ne akansu da kar su yi abota da duk wanda ba kwa so, kuma su nisanci zina.
Ya ku jama'a kuyi kyakkyawan bauta ga ALLAH (SWT) ku tsaida salloli biyar(5) na farilla, Ku Azumci Watan Ramadan ku Kuma bada zakka. Ku aikata aikin hajji in har kun sami daman yi.
KU SANI FA, ko wane musulmi dan uwan musulmi ne. Dukkan ku dai dai kuke. Ba wanda yake da fifiko saman wani sai ta tsoron ALLAH, da aikata kyawawan ayyukka. Ku tuna fa(ya ku jama'a) wata rana za ku tsaya gaban ubangijinku, domin sakamakon ayyukanku, saboda haka ku yi hattara kada ku yi sake da hanya madaidaiciya bayan na kau.
Ya ku jama'a ba wani annabi ko manzo da zai zo bayana kuma babu wani addini da zai zo (bayan addinin musulunci), saboda haka kuyi tunani sosai akan wannan magana dana gaya maku, kuma ku fahimce ta (sosai). Zan bar maku abubuwa guda biyu(2); ga (alkur ani) ga kuma (sunnah) ta. In kun bi wannan ba za ku ta ba bata ba.
Duk Wanda ya ji wannan sako to ya jiyar da wadansu, suma su jiyar da wasunsu, kuma sau da yawa wadanda za su ji magana daga karshe sufi masu ji na yanzu fahimtar abinda nake fada.
YA ALLAH ka zamo shaida agareni, cewa na isar da aikenka zuwa ga bayinka.”
Yan uwa ku watsa wannan KHUDUBAR ga yan uwa musulmi wanda kamar yau akayi ta!!!
SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM!!!

Comments

POPULAR POST

DAREN FARKO (ABUNDA YA KAMATA SABBIN MA'AURATA SUYI A SHARI'ANCE)

1. Nafarko su fara da gaisuwa irin wadda addinin muslunci ya tanadar mana (watau suyi wa junan su sallama). 2. Sai ango ya daura hannunsa a bisa goshin amaryarsa ya karanta wannan addu'ar: "Allahumma innee as'aluka min khairiha wa khairi maa jabaltaha 'alaihi wa'a uzhubika min sharriha wa sharri maa jabaltaha 'alaihi" ( Abu Dawud Ibn Maajah Al-Haakim Al-Bahaki da Abu ya'ala). 3. Daga nan sai ango da amarya su gabatar da Alwala sannan su gabatar da Sallah raka'a biyu bayan sun idar sai su karanta addu'o'i na neman 'ya'ya na gari.

MAGANIN KARFIN MAZA KO MATA A MUSULUNCE

kala-kalar abincin dake samar da karfin maza/mata  (sperm), da kuma kuzari a jikin ango da amarya. HATSI: 1. Alkama ko kuma duk wani dangin abinci da ake samarwa daga gareta. 2. Shinkafa. 3. Wake. GANYE: 1. Albasa. 2. Galik. 3. Karas. 4. Dankali. 5. Kwakwa. 'YA' YAN ITATUWA: 1. Ayaba. 2. Mangoro.

FARILLAN ALWALA, SUNNONIN ALWALA, MUSTAHABBAN ALWALA DA KUMA YADDA AKE GYARA ALWALA

F arilla alwala: niyya da wanke fuska da wanke hannaye zuwa gwiwar hannu da shafar kai da wanke kafafuwa zuwa ido-sawu da cucudawa da gaggautawa. Sunnonin alwala: wanke hannaye izuwa tsintsiyar hannu yayin farawa, da kurkure baki, da shaka ruwa, da fyacewa, da dawo da shafar kai, da shafar kunnuwa, da sabunta ruwa dan shafar kunnuwa, da jeranta farillai.

BANBANCI TSAKANIN MANIYYI, MAZIYYI, WADIYYI, DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCEN SU

Wajibine kowani baligi ko baliga su san hukunce-hukuncen su domin gyara ibadunsu. HUKUNCIN FITAR MANIYYI shine: fitowar sa tana wajabta wankan janaba akan namiji ko mace. LAUNIN MANIYYIN NAMIJI: ruwane mai kauri fari wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da zakari. Sannan yana tunkudo juna lokacin dayake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari, idan ya bushe yana kamshin kwai. LAUNIN MANIYYIN MACE: Ruwane tsinkakke, mai fatsi-fatsi, Wani lokacin kuma yana zuwa fari, wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji. Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa. Kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko damammen gari, idan ya bushe shima yana kamshin kwai. HUKUNCINFITAR MAZIYYI: hukuncin sa shine a wanke farji gaba daya, da kuma inda ya shafa, kuma a sake alwala. LAUNIN MAZIYYI: Ruwane tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar sha'awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce kakeso, ko matark...

ISTIMNA'I (masturbation) da HUKUNCIN SA

ISTIMNA'I ( masturbation) shine shine mutum ya rika wasa da al'aurassa har ya fitar da maniyyi, HUKUNCIN ISTIMNA'I Farko dai akwai hadisai wadanda suka nuna fushi na ubangiji akan mai aikata hakan, Hukuncinsa ga malaman mazhabobi guda hudu, Imam Malik Imam Shafi'i. Sun tafi akan haramta shi don haka a wurin su dole mutum yayi aure ko ya kame har zuwa lokacin da Allah zai bashi ikon yin aure.

NIYYAR WANKAN JANABA,HAIDA,NIFASI DANA JUMA'A

NIYYAR WANKAN JANABA "Bismillahi nawaitu guslul janabati farrdun raf'ul hadasil akhbari." NIYYAR WANKAN HAIDA "Bismillahi nawaitu guslul haidi farrdun raf'ul hadasil akhbari." NIYYAR WANKAN NIFASI (BIQI) "Bismillahi nawaitu guslul nifasi farrdu raf'ul hadasil akhbari." NIYYAR WANKAN JUMA'A "Bismillahi nawaitu guslul juma'ati wajibun" Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W 

WURIDIN NEMAN ARZIKI

Ga wanda ke neman arziki:  Ya yawaida karanta daya daga cikin addu'o'in nan idan kuma da hali ka karanta duka a kowace rana. Insha Allah, Allah SWT zai maka budi ta inda baka tunani. WURIDI NA FARKO: " Allahu Kafi, Allahu Ganiyyu, Allahu Fattahu, Allahu Jauwadu, Allahu Wadudu, Allahu Wasi'u, Allah Ladifu, Allahu Shahidu, Allahu Ni'imal Maula wa Ni'iman  Nasiru, Allahu yarziku man yasha'u bi gairi hisab" WURIDI NA BIYU: "Almalu walbanuna zinatul hayatud duniya, walba iyatus salihati khairun inda Rabbika thawaban wa khairun amala" Zakaja wuridin ayar nan ta sama sau dubu daya a kullum, tsawon kwana goma a kowane wata banda farkon watan Almuharram. WURIDI NA UKU: "Ka dawwama cikin karanta suratul Kahafi, Yasin, Izawaka da Tabaraka a kullum"

ZAMAN TAHIYA

Zaman Tahiya da karanta tahiya a sallah a takaice. Sallah tana kunshe da zaman tahiya guda biyu ga wanda ya samu cikakkar sallah tare da liman, Zaman tahiya da karanta tahiya sunna ne mai karfi a sallah. Tahiya ta farko a sallah: Ana takaituwa akan lafazin tahiya ne a zama na farko. Tahiya ta biyu a sallah: A zaman tahiya na biyu a sallah ana karawa akan lafazin tahiya da salati ga annabi da alayensa wanda imamu Malik ya tafi akan cewa kana iya takaituwa da salatin Annabi koda ba hada da alayensa ba kuma sallah tayi. Imam shafi'i kuma ya tafi akan cewa wajibine ka hada da alayensa. Sannan kuma akwai addu'o'in neman tsari da wuta da kuma Dujjal ga wanda Allah yaba ikon haddacesu. Sallama a sallah farali ne sannan zaman da zakayi na gwargwardon fitar lafazin sallamar shima farali ne. Ku kasance tare damu domin kawo muku Lafazin tahiya da salatin Annabi da kuma adduar da ake bayan salatin. Wallahu ta'ala a'alam. Salati 10 ga Ann...

TARJAMAR JAUHARA DA HAUSA

Allahumma salli wa sallim ala ainirrahmatir rabbaniyati wal yaqutatul mutahaqqiqatul ha'idati bimarkazil fuhumi wal  ma'aniy wannuril akwanil mutakawwinatul adamiyyi sahibul haqqir rabbani albarqil asda'i bimuzunil arbahil mali'ati likulli muta arridin minal buhuri wal awani wannuri kalami'illazi mala'ata bihi kaunikal ha'ida bi amkinatil makani allahumma salli wa sallim ala ainil haqqillati tatajalla minha  urushul haqa'iqil ainil ma'arifi siradika Tamil asqam Allahumma salli wa sallim ala dal'atil haqqi bil haqqi kanzil  aazam ifada tuka minka ilaika ha'idatun nurul mudalsam sallahu alaihi wa ala alihi salatan tu'arrifuna Biha iyyahu.  - DAGA MALAM IBRAHIM ALIYU MAI DIWANI Salati 10 ga Annabi S.A.W