Wannan kuwa shine Hadisin da Bukhari Da Muslim suka ruwaito cewa:
Manzon Allah S.A.W. Ya ce: "Mai ZINA ba ya yin ZINA a lokacin da yake yin ZINA A halin
yana da IMANI, haka nan BARAWO ba yin sata a lokacin da yake SATA a halin yana Mumini, Haka kuma Mashayin GIYA ba zai sha GIYA ba a lokacin da yake shan GIYA a halin yana Mumini. Kuma mai kwace ba zai kwace kayan wani ba, kayan da Mutane za su daga ido su Kyale shi saboda mamakin taurin zuciyarsa a halin yana matsayin Mumini, Haka nan mai Satar ganima ba zai sace ganima ba a halin yana matsayin Mumini.

Saboda haka ku yi hankali da kanku ku yi hankali da Kanku.
Haka ya zo a cikin Littafin Almishkat' a Babin Alkaba'ir.
Ya Dan'UwaNa/ 'Yar'UwaTa a cikin Soyayyar Allah Da Manzon Sa S.A.W. Wadannan ayyukan da aka ambata a cikin Hadisin Bukhari da Muslim suka ruwaito shi, Ko da yake dai kanana ne a idon ka/ki, Kuma sai dai a bar su saboda tsoron Allah kuma domin fifita lahirarka a kan duniyarka lallai Allah Zai gafarta maka, saboda la'akari da fadin Allah
Madaukakin Sarki
Madaukakin Sarki
"AMMA KUMA DUK WANDA YA JI TSORON TSAYAWA A GABAN UBANGIJISA, KUMA YA HANA ZUCIYARSA TA AIKATA ABIN DA TAKE SO TO LALLAI ALJANNA ITA CE MAKOMA {A WAJENSA}." Surah Nazi'at 40-41.
Wannan kuwa ba ya sabawa da cewa, duk wanda ya yi shishshigi kuma ya saba wa Umarnin Allah ya fifita rayuwar duniya a kan ta lahira sannan bai hana zuciyarsa aikata abin da take so ba, to wannan makomarsa ita ce "JAHANNAMA". Saboda aikata wannan mummunan aiki. Lallai Allah Ya yi Gaskiya da Yakecewa:
"DUK WANDA YA YI SHISHSHIGI KUMA YA FIFITA RAYUWAR DUNIYA A KAN TA LAHIRA TO LALLAI WUTAR JAHANNAMA ITA CE MAKOMA". Surah Nazi'ar 38-39.
Allah Ya Kiyaye Mu Daga Wannan Abu. Ameen
Salati 10 ga Annabi S.A.W
Comments
Post a Comment