Ya
iganta imaninsa sannan yasan abinda zai kyautata farillan aininsa da shi, kamar
ilimin hukunce-hukuncen sallah da tsarki da azumi.
Ya
wajaba a kansa ya kiyaye iyakokin ALLAH tsarkakken Sarki tun baiyi azaba a gare
shi ba.
Ya
wajaba a kansa ya kiyaye harshensa daga maganganu na sabo da munanan maganganu
da duk wani zance mara dadi, ya kiyaye harshensa daga rantsuwa da sakuwar
matsarsa, ya nisanci yin barazana ga musulmi da walakantashi, da zaginsa da
tsorata shi ba tare da hakkin shari’a ba.
Ya
wajaba a kansa ya kiyaye ganinsa daga kallon haramun, bai halatta ba a gare shi
ya kalli musulmi da irin kallon da zai cuce shi, sai dai idan musulmin mai
yawan sabo ne a fili, toh wannan ya zama dole ya kaurace masa.
Ya
wajaba a kansa ya kiyaye dukkanin gabbansa iyakar ikonsa. Ya yi soyayya don
ALLAH, ya yi kiyayya don ALLAH, ya yarda da mutum saboda ALLAH, ya yi fushi don
ALLAH, ya rika yin umarni da kyawawan aiki, ya yi hani ga barin mummunan aiki.
Karya
ta haramta a gare shi, da giba, da annamimanci, da girman kai da kaye, da riya,
da jiyarwa, da hassada, da gaba, da ganin fifiko akan wani, da yafice, da
zunde, da wasa, da izgili, da zina, da kallon mace ajnabiyya, da jin dadin
firarta, da cin dukiyar mutane ba tare da dadin rai ba, da ci da sunan ceto ko
da sunan addini, da jinkirta sallah ga barin lokutanta.
Bai
halatta a gare shi ba yayi abota da fasiki, ko ya zauna da shi in dai bada
lalura ba, kada ya nemi yardar halatta a cikin abinda zai sabawa ALLAH
Mahalicci.
ALLAH
mai tsarki da daukaka ya ce : ( ALLAH da MANZONSA su ne suka fi wajaba mutane
su nemi yardarsu indai sun kasance masu imani ) Suratul-Tauba 621.
Mai
tsira da amincin ALLAH ya ce: “babu biyayya ga wani abin halitta a cikin sabon
mahalacci”
Bai
halatta ba a gare shi ya yi wani aiki har sai ya san hukuncin ALLAH a cikinsa,
(idan bai sani ba) ya tambayi malamai, ya yi koya da masu bin Sunnar ANNABI
MUHAMMADU (S.A.W), wadanda suke shiryawa ga bin ALLAH TA’ALA, masu tsoratawa ga
barin bin shaidan, kada ya yardarwa kansa irin abinda ababan fallasa suka yarda
dashi, wadanda rayuwarsu ta tozarta a cikin bin wanin ALLAH TA’ALA, ya girman
asarar irin wadannan mutane, ya tsawan kukansu ranar Alkiyama”.
Muna
rokon ALLAH yayi mana mawafaka ga bin Sunnar ANNABINMU MACECINMU SHUGABANMU
MUHAMMADU S.A.W.s