Skip to main content

Posts

Showing posts from April, 2014

KADAN DAGA YADDA BILAL YAKE SON SHUGABA S.A.W

WANI LAMARI MAI GIRGIZA ZUCCIYAR MASOYAN ANNABI MUHAMMADU S.A.W YA FARU BAYAN WAFATINSA yayinda sayyiduna Bilal yaga damuwa da kadaicin rabuwa da babban masoyinmu ya tsananta gareshi madina ta zamemashi tamkar keji abu ya zamo ko kiransallah baya iyayi domin da ya kawo wurin "ASH HADU ANNA MUHAMMADURRASULULLAH" sai yaji muryarsa ta shake ta tsaya don kuka da kaunar annabi S.A.W gani yake kamar zai waiwaya yagansa . Da yaga abu yatsananta gareshi saiya nemi iznin khalifa sayyiduna Abubakar Assaddiq R.A don ya tashi ya koma kasar Sham ya zauna acan tareda wasu cikin sahabban manzon Allah. 

HADISI MAI BAN TSORO

Wannan kuwa shine Hadisin da Bukhari Da Muslim suka ruwaito cewa:  Manzon Allah S.A.W. Ya ce: "Mai ZINA ba ya yin ZINA a lokacin da yake yin ZINA A halin yana da IMANI, haka nan BARAWO ba yin sata a lokacin da yake SATA a halin yana Mumini, Haka kuma Mashayin GIYA ba zai sha GIYA ba a lokacin da yake shan GIYA a halin yana Mumini. Kuma mai kwace ba zai kwace kayan wani ba, kayan da Mutane za su daga ido su Kyale shi saboda mamakin taurin zuciyarsa a halin yana matsayin Mumini, Haka nan mai Satar ganima ba zai sace ganima ba a halin yana matsayin Mumini. Saboda haka ku yi hankali da kanku ku yi hankali da Kanku. Haka ya zo a cikin Littafin Almishkat' a Babin Alkaba'ir.

YADDA AKE WANKAN JANABA

Kamar yadda yazo daga sheikh DAN ALMAJIRI kano Da farko za'a fara gusar da najasa sannan sai a wanke alqalami sannan sai ayi niyya kamar haka:  "BISMILLAHI NAWAITU GUSLUL JANABATI FARRDUN RAFA'UL HADASUL AKHBAR." sannan a wanke kai sau ukku(3) a chachchakuda a yayin wanke kan sannan a koma a wanke gabban alwala sau dai dai(1) sannan sai a tsaga jiki ya zuwa kaso biyu(2) a wanke kowane kaso daga ciki, gaba ya zuwa gaba, daga sama zuwa qasa daga qarshe idan an gama sai kace:  "ALHAMDULILLAHILLAZI ZAHABA ANNIL'AZA WA'AFANI." ma'ana: godiya ta tabbata ga UBANGIJIN daya tafiyar mani da qazanta ya bani lafiya. ALLAH YASA MU DACE AMEEN. Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W 

NIYYAR WANKAN JANABA,HAIDA,NIFASI DANA JUMA'A

NIYYAR WANKAN JANABA "Bismillahi nawaitu guslul janabati farrdun raf'ul hadasil akhbari." NIYYAR WANKAN HAIDA "Bismillahi nawaitu guslul haidi farrdun raf'ul hadasil akhbari." NIYYAR WANKAN NIFASI (BIQI) "Bismillahi nawaitu guslul nifasi farrdu raf'ul hadasil akhbari." NIYYAR WANKAN JUMA'A "Bismillahi nawaitu guslul juma'ati wajibun" Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W 

MUKE JAWA KANMU

Kar Ka Yarda Wani Ya Rude Ka Da Cewa Wai Duk Fituntunun Da Muke Fuskan Ta wai Gwamnati Ce Ko Goodluck Ne Ko Wanene Ko Wanene A'a Ba Haka Bane Ga Yadda Abin Yake Wallahi Mun Saki Allah Ne !!! Mun Bar Umarnin Allah !!! Wallahi Malam Mun Saki Umarnin Allah Da MukaYi Alkawarin Dauka Ne Yau Idan Ka Duba wa'annan Abubuwan Da Zan Lissafo Sun Zama Ruwan Dare A Wajen Musulmai Amma Banda Muminai Ma'ana Muminai Basa Aikatawa Su 1. Zina 2. Madigo 3. Luwadi 4. Sata

KHUDUBAR ANNABI MUHAMMAD(S.A.W) TA RANAR TARA GA WATAN ZUL-HIJJAH

KHUDUBAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM WANDA YAYI A KHUDUBAR RANAR TARA GA WATAN ZUL - HIJJAH , SHEKARA TA GOMA DA HIJIRA A DUTSEN ARAFAT (RANAR ARFA KENAN). ANNABI (SAW)YA FARA DACEWA: “Ya ku mutane ku bani hankalinku, domin mai Yiwuwa bazan sake kasancewa da ku bayan wannan shekaran ba, saboda haka ku saurari abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar da abinda zan gaya maku) ga wadanda basa wannan wuri a yau. Ya ku mutane kamar yadda kuka riki wannan wata, (na hajji) da wannan rana (ta arfa) da kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma abin tsarewa, to, haka kuma ku riki Ran Musulmi da kuma Dukiyoyinsu da girma abin kuma karewa, ku maida wa Mutane kayan da suka baku Amana. Kar ku cuci kowa, saboda kar wasu su cuce ku, ku tuna fa, hakika ALLAH zai yi sakayya akan ayukakanku, ALLAH (SWT) ya hana cin riba,(wato kudin ruwa) saboda haka, duk abin da aka kulla ta kudin ruwa sai a warware shi. Ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye Addininku. Yanzu kan ya fidd...

HADITH NA DAYA

Hadisi na farko daga littafi mai albarka na imamu Muhyiddin abu zakariyya, yahya dan sharafu annawawy Allah yai rahma agareshi madawwamiya. Ana kiran wannan littafi da Arba'inannawawy, saboda dan ganta sunan zuwa ga wanda yarubutashi(shine imamu annawawy) kuma nasabarsa(nawawy). Sannan malam Ahmad dan Abdurrahman dan rajab ya qara Hadisi takwas(8) daga cikin wannan littafi saboda haka suka zama hadisai hamsin kenan. Malamai dayawa sunyi sharhin wannan littafi, a cikinsu akwai sharhin Ahmad dan Abdurrahman dan Rajab a cikin littafinsa mabayyani mai suna(Jami'ul Uluumi Wal Hikami). Daga qarshe muna rokon Allah ya bamu ikon yin wannan aiki mai girma da muka dauko. ( HADISI NA FARKO ) An karbo wannan hadisi daga sarkin muminai , baban Hafsin Umar dan Kaddabi Allah ya qara yarda agareshi ameen . Yace ! naji MANZON ALLAH ( S.A.W ) yana cewa : Lallai dukkan ayyuka basu tabbata saida niyya , kuma yana ga dukkan kowane mutum abunda yai niyya , wan...

TAFARKIN TSIRA

ANNABI (SAW) yana cewa: Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Yaa Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani. Kasa mucika da imani.

LADUBBAN SALLAMA

1. Mustahabi ne idan anyi sallama a hada hannu. Annabi(saw) yace wanda suka hada hannu za'a gafar ta musu zunuban su. 2. Kuma anfi so mutum ya fara gaisawa da mutane daga hannun daman sa. 3. Bayan mutum zai bar cikin mutane zai sake yin sallama. Manzon Allah (saw) yace tafarkon ba tafi ta karshen ba, ma'ana ladan su iri dayane. 4. Wanda yake tafiya shi zai yiwa na zaune, wanda yake kan abin hawa yayi wa mai tafiya. Wanda ya fara yin sallama lokacin da aka hadu shi yafi samun falala. 5. Ko kasan mutum ko bakan sanshi ba za kayi masa sallama. 6. Namiji zai iya yiwa mace, mace ma zata iya yiwa namiji sai de a kyautata niya. 7. Amma masu cewa Salamu'alaikum wannan ba sallama bace hausane kawai, amma yazo acikin Alqur'ani za ka iya cewa Salamun'alaikum. Hukunce-hukuncesallama yana da yawa mutum ya duba AL-ADABUL MUFRAD na Imamul Bukhari don karin bayani Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W 

NIYYAR YANKAN LAYYAH DAGAGIDAN ANNABI (SAW)

ﻣﻦ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻟﻤﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﺃﻥ ﻳﺬﺑﺢ ﺍﻷﺿﺤﻴﺔ yanadaga sunnar ma'aiki gawanda yake da niyyar yanka layyarsa, ﺃﻥ ﻳﻘﻮﻝﻋﻨﺪ ﺍﻟﺬﺑﺢ yafadi wannan kalmar lokacin da zaiyi yanka. ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻫﺬﺍ ﻣﻨﻚ ﻭﻟﻚ ، ﻫﺬﺍ ﻋﻨﻲ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺗﻘﺒﻞ ﻣﻨﻲ ) IDAN KUMA WANI ZAKA YANKAWA SAI KACE

NIYYAR WAZIFA,ZIKIRIN JUMA'A,LAZIMIN SAFE DA YAMMA

NIYYAR LAZIMIN SAFE Allahumma inni nawaitu an ata qarraba ilaika bi qira'ati wurdissabahil lazimi fi darikatil tijjaniyati iktida'a bi sayyadi Ahmad Tijjani RTA ta'abudan lillah. NIYYAR LAZIMIN YAMMA Allahumma inni nawaitu an ata qarraba ilaika bi qira'ati wurdil masa'i allazimi fi darikatil tijjaniyati iktida'a bi sayyadi Ahmad Tijjani RTA ta'abudan lillah. NIYYAR WAZIFA Allahumma inni nawaitu an ata qarraba ilaika bi qira'atil wazifatil tijjaniyati iktida'a bi sayyidina Ahmad tijjani RTA ta'abudan lillah NIYYAR ZIKIRIN JUMA'AT Allahumma inni nawaitu an ata qarraba ilaika bi tilawati hailalati juma'ati allazimati fi darikatil tijjaniyati iktida'a bi sayyadi Ahmad Tijjani RTA ta'abudan lillah.

ADADIN LAZIMIN SAFE DA YAMMA

ADADIN LAZIMIN SAFE 1.Istigfari         100 2.Salatul fatihi     100 3.Hailalah         100 ADADIN LAZIMIN YAMMA 1.Istigfari       100 2.Salatul fatihi   100 3.Hailalah       100

FASSARAR JAUHARA A TAKAICE

Kashi na 1 Allah kayi tsira da Aminci a bisa ainihin rahamar Ubangiji, kuma wanda yake shine (ya'aqut) na gaskiya Shi ya'aqut wani ma'adanine wanda yafi dukkan ma'adanai tsada don haka aka kamantashi da manzon Allah don manzon Allah shine yafi komai tsada Duniya da Lahira Wannan tsadar itace ta zamanto matattarar dukkan ilimomi na zahiri da badini Kuma shine hasken duk wani abin halitta wanda yake daga Annabi Adam Kuma ma'abocin gaskiya wanda yake gaban dukkan kowa a fadar ubangiji Haske wanda ya hudo ko ya fito da ma'aunoni na ribobi wadanda suke cike da  rahamomi ga dukkan zukatan da suke cike da zikiri na waliyan Allah da bayi salihai Kuma haskene wanda dashine Allah ya haskakawa bayinsa suka gane hanya madaidaiciya dashi wanda yake tattare da dukkan girma na matsayi.

TARJAMAR JAUHARA DA HAUSA

Allahumma salli wa sallim ala ainirrahmatir rabbaniyati wal yaqutatul mutahaqqiqatul ha'idati bimarkazil fuhumi wal  ma'aniy wannuril akwanil mutakawwinatul adamiyyi sahibul haqqir rabbani albarqil asda'i bimuzunil arbahil mali'ati likulli muta arridin minal buhuri wal awani wannuri kalami'illazi mala'ata bihi kaunikal ha'ida bi amkinatil makani allahumma salli wa sallim ala ainil haqqillati tatajalla minha  urushul haqa'iqil ainil ma'arifi siradika Tamil asqam Allahumma salli wa sallim ala dal'atil haqqi bil haqqi kanzil  aazam ifada tuka minka ilaika ha'idatun nurul mudalsam sallahu alaihi wa ala alihi salatan tu'arrifuna Biha iyyahu.  - DAGA MALAM IBRAHIM ALIYU MAI DIWANI Salati 10 ga Annabi S.A.W