TSARKI YA KASU KASHI BIYU: Tsarkin kari da tsarkin dauda, gaba dayansu ba sa inganta sai da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa, shine wanda launinsa bai jirkita ba da basa haduwa da shi a bisa hali mafi yawa, kamar misalin narkakken mai da sandararren mai da romo gaba dayansu da shuni da sabulu da dauda da makamancinsu, babu laifi idan ya hadu da tulbaya da kasar kanwa da kasar gishiri da jar kasa da makamancinsu. FASALI: idan najasa ta ayyana (wato aka san wurin da take) sai a wanke wurinta, idan ta rikitar sai a wanke tufan gaba dayansa