Skip to main content

Posts

Showing posts from October, 2014

Sayyiduna Uthman bn Affaan (ra) yace

Mutumin da yasan Allah, sani NA HAQIQA, yana da wasu alamomi guda takwas (wadanda ake ganeshi dasu). 1 & 2. Zuciyarsa zata kasance cike da tsoron Azabar Allah, da kuma kwadayin rahamarsa. 3&4. Harshensa zai kasance ko yaushe cikin furta yabo ga Allah, da kuma bayyana gidiyarsa gareshi. 5&6. Idanuwansa zasu kasance ko yaushe cikin Jin kunyar Ubangijinsa, da kuma Zubda hawaye cikin tunaninsa. 7&8. Zai kasance cikin Burin rabuwa da duniya ako yaushe, da kuma neman yardar Ubangijinsa. Ya Allah ka azurtamu da wadannan Halayen. Fatiha da salati 10 ga SHUGABA S.A.W. 

DARAJOJI GUDA 10 GAME DA SAYYIDUNA UTHMAN BN AFFAN (rta)

DARAJOJI GUDA 10 GAME DA SAYYIDUNA UTHMAN BN AFFAN (rta) Kafin mutuwar Shahadarsa, Sayyiduna Uthman (ra) ya gaya ma ABU THAWR AL- FAHMIY cewa: "Ina Kyautata zato awajen Ubangijina saboda wasu abubuwa guda goma wadanda na sanyasu amatsayin amana tsakanina dashi. Abubuwan sune: 1. Nine mutum na hudu wajen shiga Musulunci. 2. Manzon Allah (saww) ya aura min 'Yarsa ta cikinsa. 3. Da ta mutu ya Qara aura min da 'Yar uwarta. 4. Tunda nake ban ta'ba rera waka ba. 5. Tunda nake ban ta'ba Tunanin aikata mugunta ba. 6. Tun daga ranar da nayi mubaya'a ga Manzon Allah (saww) da hannuna na dama, ban sake shafar al'aurata da wannan hannun ba.

SAYYIDUNA ALIYYU bn ABI TALIB (ra) yace

"Watarana Mun fita Gefen Garin Makkah tare da Manzon Allah (saww).  «Bayan Fat'hu Makkah». Amma babu wasu Duwatsu ko Bishiyoyi da muka wuce ta kusa dasu fache sai munji suna cewa: "ASSALAMU 'ALAIKA YA RASULALLAHI" «Aduba Sunanut Tirmidhy hadisi na 3,646» Allahu Akbar! Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W 

A MOST READ HADITH

Watarana Manzon Allah (saww) ya hau kan DUTSEN UHUDU tare da Sayyiduna Abubakar (ra) da Sayyiduna Umar (ra) da Sayyiduna Uthman (ra). Sai Dutsen ya fara girgiza. Sai Manzon Allah (saww) yace: "KA NUTSU YA UHUDU!! ANNABI NE AKANKA TARE DA SIDDIQI GUDA DAYA, DA KUMA SHAHIDAI GUDA BIYU". (Sahihul Bukhary Juz'i na 5 shafi na 24). Wannan hadisin ma yana ishara ne shima izuwa ga ILIMIN GAIBU irin wanda Allah ya sanar da Manzonsa (saww). Kunga acikin wannan hadisin Manzon Allah (saww) ya bada labarin cewa : ★ SAYYIDUNA ABUBAKRIN SIDDIQI NE. ★ SAYYIDUNA UMAR DA UTHMAN SHAHADA ZASUYI. ★ YANA MAGANA DA DUWATSU, KUMA SUNA JIN MAGANARSA (SAWW).

ZAMAN TAHIYA

Zaman Tahiya da karanta tahiya a sallah a takaice. Sallah tana kunshe da zaman tahiya guda biyu ga wanda ya samu cikakkar sallah tare da liman, Zaman tahiya da karanta tahiya sunna ne mai karfi a sallah. Tahiya ta farko a sallah: Ana takaituwa akan lafazin tahiya ne a zama na farko. Tahiya ta biyu a sallah: A zaman tahiya na biyu a sallah ana karawa akan lafazin tahiya da salati ga annabi da alayensa wanda imamu Malik ya tafi akan cewa kana iya takaituwa da salatin Annabi koda ba hada da alayensa ba kuma sallah tayi. Imam shafi'i kuma ya tafi akan cewa wajibine ka hada da alayensa. Sannan kuma akwai addu'o'in neman tsari da wuta da kuma Dujjal ga wanda Allah yaba ikon haddacesu. Sallama a sallah farali ne sannan zaman da zakayi na gwargwardon fitar lafazin sallamar shima farali ne. Ku kasance tare damu domin kawo muku Lafazin tahiya da salatin Annabi da kuma adduar da ake bayan salatin. Wallahu ta'ala a'alam. Salati 10 ga Ann...