4 Jan 2016

JANABA TA KASU KASHI BIYU

na farko shine fitar maniyyi ta hanyar jin dadi na al'ada, a bacci ko a farke, ta hanyar jima'i ko waninsa.

Na biyu shine buyan hashafa (wato kan azzakari) a cikin farji.

Wanda yayi mafarki yana tarawa da mace amma maniyyi bai fito masa ba, to babu komai a kansa.

Wanda ya samu busasshen maniyyi a jikin tufansa bai san yaushe ne ya same shi ba, to yayi wanka ya sake abunda ya sallata tun daga baccin sa na qarshe da yayi da wannan tufan.Wanka yana wajaba saboda abubuwa uku sune: Janaba, Haila da Nifasi

Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W

No comments:

Post a Comment