19 Jan 2016

HUKUNCIN YIN JIMA'I DA AMARYA KO UWARGIDA TA DUBURA

Kamar yadda shari'a tayi hani akan aiwatar da jima'i ga uwargida ko amarya a lokacin da take haila, hakama jima'i ta dubura shari'a tayi hani mai tsanani akan aiwatar dashi.

MANZON ALLAH (S.A.W) yayi hani ga wadannan munanan aiyuka (jima'i a lokacin haila da jima'i ta dubura) a Hadisai da dama.

MANZON ALLAH  (S.A.W) yace: mutumin dake jima'i da matarsa ta dubura ALLAH Madaukakin Sarki ba zai dube shi da tausayi ba a ranar karshe.

Shehun malami Imam Ghazzali (R.A) ya rubuta a cikin littafinsa "IHYA" cewa yin jima'i da mace ta dubura yafi laifi mai tsanani akan yin jima'i da ita yayin da take haila. (A sani dukkansu laifukane masu tsanani)Shi kansa namiji abin na haifar masa da cututtuka wadanda zasu iya gurgunta masa rayuwa, ko kuma suyi sanadiyyar ajalinsa.

manyan likitocin zamani sunyi bincike sun gane cewar akwai babbar matsalar tattare da yin jima'i da mace ta dubura. Saboda haka nake kira gareku 'yan uwa na Musulmai mu kiyaye sannan mubi ALLAH S.W.T da MANZON sa S.A.W

ALLAH S.W.T ne masani
Salati 10 ga Annabi Muhammad S.A.W

No comments:

Post a Comment