Skip to main content

Sayyiduna Abubakrin R.A

Sayyiduna Abubakrin bai fifici sauran Sahabbai da yawan Sallah ko yawan Azumi, ko yawan Ruwayar Hadisai ba. Sai dai ya Fificesu ne da Yawan Soyayyar Manzon Allah (S.A.W.W).
Wannan Soyayyar ta sanya ba ya ganin komai agabansa sai Allah da Manzonsa (S.A.W.W).
Kuma wannan Soyayyar ce ta sanyashi yake da saurin Gaskatawa da zarar wani Umurni ko hani ya sauka.
Wannan Soyayyar ce ta sanya Allah ya zabeshi ya zama Khalifan farko daga cikin Khalifofin Masoyinsa (S.A.W.W).
Haka nan shima Manzon Allah (S.A.W.W) yana mutukar Qaunar Sayyiduna Abubakar (R.A).
Har Watarana Sayyiduna Amru bn Al-aas (R.A) ya tambayi Manzon Allah (S.A.W.W) Wanene Wanda kafiso acikin Mutane baki dayansu?"
Sai yace masa "A'isha".
Sai yace "Acikin Maza fa?"
Sai yace "Abubakar ne".
Mutane sukan fuskanci bacin rai sosai daga Manzon Allah (S.A.W.W) aduk lokacin
da suka 'bata ran Sayyiduna Abubakrin.
Wannan Qarfin Soyayyar ce ta sanya Sayyiduna Abubakrin yafi kowa Imani
daga cikin wannan al'ummar.

Comments

POPULAR POST

MAGANIN KARFIN MAZA KO MATA A MUSULUNCE

kala-kalar abincin dake samar da karfin maza/mata  (sperm), da kuma kuzari a jikin ango da amarya.
HATSI: 1. Alkama ko kuma duk wani dangin abinci da ake samarwa daga gareta. 2. Shinkafa. 3. Wake.

GANYE:
1. Albasa.
2. Galik.
3. Karas.
4. Dankali.
5. Kwakwa.

'YA' YAN ITATUWA:
1. Ayaba.
2. Mangoro.

DAREN FARKO (ABUNDA YA KAMATA SABBIN MA'AURATA SUYI A SHARI'ANCE)

1. Nafarko su fara da gaisuwa irin wadda addinin muslunci ya tanadar mana (watau suyi wa junan su sallama).

2. Sai ango ya daura hannunsa a bisa goshin amaryarsa ya karanta wannan addu'ar:

"Allahumma innee as'aluka min khairiha wa khairi maa jabaltaha 'alaihi wa'a uzhubika min sharriha wa sharri maa jabaltaha 'alaihi"
( Abu Dawud Ibn Maajah Al-Haakim Al-Bahaki da Abu ya'ala).

3. Daga nan sai ango da amarya su gabatar da Alwala sannan su gabatar da Sallah raka'a biyu bayan sun idar sai su karanta addu'o'i na neman 'ya'ya na gari.

FARILLAN ALWALA, SUNNONIN ALWALA, MUSTAHABBAN ALWALA DA KUMA YADDA AKE GYARA ALWALA

Farilla alwala: niyya da wanke fuska da wanke hannaye zuwa gwiwar hannu da shafar kai da wanke kafafuwa zuwa ido-sawu da cucudawa da gaggautawa.
Sunnonin alwala: wanke hannaye izuwa tsintsiyar hannu yayin farawa, da kurkure baki, da shaka ruwa, da fyacewa, da dawo da shafar kai, da shafar kunnuwa, da sabunta ruwa dan shafar kunnuwa, da jeranta farillai.

ISTIMNA'I (masturbation) da HUKUNCIN SA

ISTIMNA'I ( masturbation)

shine shine mutum ya rika wasa da al'aurassa har ya fitar da maniyyi,

HUKUNCIN ISTIMNA'I

Farko dai akwai hadisai wadanda suka nuna fushi na ubangiji akan mai aikata hakan,
Hukuncinsa ga malaman mazhabobi guda hudu,

Imam Malik Imam Shafi'i.
Sun tafi akan haramta shi don haka a wurin su dole mutum yayi aure ko ya kame har zuwa lokacin da Allah zai bashi ikon yin aure.

HUKUNCIN YIN JIMA'I DA AMARYA KO UWARGIDA TA DUBURA

Kamar yadda shari'a tayi hani akan aiwatar da jima'i ga uwargida ko amarya a lokacin da take haila, hakama jima'i ta dubura shari'a tayi hani mai tsanani akan aiwatar dashi.

MANZON ALLAH (S.A.W) yayi hani ga wadannan munanan aiyuka (jima'i a lokacin haila da jima'i ta dubura) a Hadisai da dama.

MANZON ALLAH  (S.A.W) yace: mutumin dake jima'i da matarsa ta dubura ALLAH Madaukakin Sarki ba zai dube shi da tausayi ba a ranar karshe.

Shehun malami Imam Ghazzali (R.A) ya rubuta a cikin littafinsa "IHYA" cewa yin jima'i da mace ta dubura yafi laifi mai tsanani akan yin jima'i da ita yayin da take haila. (A sani dukkansu laifukane masu tsanani)