HUKUNCIN HAYAR MAHAIFA, DA SAYAR, KO KYAUTAR DA KWAYOYIN HALITTA A MUSULUNCI KASHI NA UKU 2 - Hukuncin idan matar da aka ari mahaifarta ta zamo kishiyar mai kwayoyin halitta: Mun bayyana cewa malaman Shari’ar Musulunci sun hadu akan haramci bayar da hayar mahaifa, idan mai mahaifar ba ta da dangantaka ta aure da namijin da aka hada maniyyin sa da kwayoyin halittar da aka ciro daga maniyyin matarsa.. Haka ma haramun ne a hada maniyyin namiji da kwayoyin halittar wata macen da ba matarsa ba; domin a shigar a cikin mahaifar matarsa.. Amma idan matar da za ta bayar da mahaifar tata kishiya ce ta mai kwayoyin halittar, ma’ana: matan mutum daya ne, mijinsu daya, to a nan malamai sun yi sabani; wasu suna ganin babu laifi a yi hakan saboda lalura, ganin cewa dukansu matan mutum daya ne. Wasu malaman kuma suna ganin cewa hakan haramun ne, domin ba shi da wani bambanci da surar farko da muka bayyana.. “al-Majma’ul Fiqhiy al-Islamiy”: wato Kungiyar masana ilimin Fiqhun Musulunci sun zartar da