Skip to main content

Posts

Showing posts from January, 2016

HUKUNCIN YAWAN KOKONTO A CIKIN SALLAH

mai yawan shakku shine yayi kokari wajan yin sallah cikin jama'a wato tare da liman, Idan haka bata samuba sai ya lura da kokonton Nasa dadine ko ragi Idan ragine sai yazo da abunda ya rage sai yayi sujjada ba'adi, Idan karine sai yayi sujjada ba'adassalami shima. Kasani/kisani cewa mai mantuwa kashi Uku ne. 1- Wanda ya manta ko ya kara cikin wani Abu na farillah. Wannan dole sai yazo da Abunda ya rage Idan yakai matsayin farillah dole sai yacikoshi sai yayi sujja bayan sallama Idan ya bai tunaba har saida ya sallame Kuma Aka samu lokaci sallar ta baci sai ya sake Idan kuma ya tuna a kusa sai ya kawo Abunda ya rage yayi sujjada bayan sallama.

HUKUNCIN YIN JIMA'I DA AMARYA KO UWARGIDA TA DUBURA

Kamar yadda shari'a tayi hani akan aiwatar da jima'i ga uwargida ko amarya a lokacin da take haila, hakama jima'i ta dubura shari'a tayi hani mai tsanani akan aiwatar dashi. MANZON ALLAH (S.A.W) yayi hani ga wadannan munanan aiyuka (jima'i a lokacin haila da jima'i ta dubura) a Hadisai da dama. MANZON ALLAH  (S.A.W) yace: mutumin dake jima'i da matarsa ta dubura ALLAH Madaukakin Sarki ba zai dube shi da tausayi ba a ranar karshe. Shehun malami Imam Ghazzali (R.A) ya rubuta a cikin littafinsa "IHYA" cewa yin jima'i da mace ta dubura yafi laifi mai tsanani akan yin jima'i da ita yayin da take haila. (A sani dukkansu laifukane masu tsanani)

WANKAN JANABA (FARILLAI, SUNNONI DA MUSTAHABI) DA HUKUNCI A CIKIN WANKAN

FARILLAN WANKA: Yin niyya yayin farawa da gaggautawa da cuccudawa da gama jiki da ruwa. SUNNONIN WANKA: Wanke hannaye ya zuwa tsintsiyar hannu kamar yadda akeyi a alwala, da kurkure baki, da shaka ruwa, da fyacewa, da wanke kofar kunnuwa itace kofa mai shiga cikin kai, amman fatar kunne wajibine a wanke cikinta da bayanta. MU SAHABBAN WANKA: Farawa da wanke najasa, sannan a wanke azzakari inda a nan ne zaiyi niyyar wankan, sannan ya wanke gabban alwala sau dai-dai, sannan ya wanke saman jikinsa, da wanke kai sau uku da gabatar da tsagin jikinsa na dama, da karanta ruwa akan gabbai. HUKUNCE HUKUNCEN WANKA

RANAKU DA LOKUTTAN DA ANSO A GABATAR DA JIMA'I A CIKINSU

Ranaku da aka so ango ya gabatar da jima'i  da amaryarsa, domin fa'ida da samun falalarsu. Daren litinin, ana samun mahaddacin Alkur'ani. Daren talata, ana samun yaro/yarinya Shahidi. Daren alhamis, ana samu yaro/yarinya mai yawan tsoron ALLAH S.W.T, ko kuma wayayye mai kwarjini. Ranar juma'a kafin a tafi sallar Juma'a,  ana samun yaro/yarinya mai sa'a tare da samun kyakkyawan karshe. Jima'i a daren Juma'a na da matukar kyau domin shine mafi darajar darare guda bakwai. Annabi S.A.W yace:

JANABA TA KASU KASHI BIYU

na farko shine fitar maniyyi ta hanyar jin dadi na al'ada, a bacci ko a farke, ta hanyar jima'i ko waninsa. Na biyu shine buyan hashafa (wato kan azzakari) a cikin farji. Wanda yayi mafarki yana tarawa da mace amma maniyyi bai fito masa ba, to babu komai a kansa. Wanda ya samu busasshen maniyyi a jikin tufansa bai san yaushe ne ya same shi ba, to yayi wanka ya sake abunda ya sallata tun daga baccin sa na qarshe da yayi da wannan tufan.

NIYYAR GABATAR DA JIMA'I

GABATAR DA ADDU'O'I KAFIN JIMA'I Domin neman tsari daga shaidanu da kuma wasu illoli, anso lokacin da ango ke jima'i da amaryarsa ya karanta wannan addu'o'i,  ta wannan hanya ango da amarya zasu samu tsari. "Bismillahi Allahumma jannibnash shaidana wa jannibish shaidana ma razaktana" A lokacin da ango zai inzali (wato zai kawo maniyyi) zai karanta wannan addu'ar "Allahumma lataja alli shaidana fiimaa razaktana nasiiba." Wadannan  addu'o'i na da matukar Muhimmanci ga ango da amarya, don haka nake kira ga sabon ango yayi kokarin haddace wadannan addu'o'i kuma yayi kokarin koyawa amaryar in har bata iya ba.

ABUBUWAN DA AKA HARAMTA MARA ALWALA YI

Salla, tawafi, shafar Al-Qur'ani mai girma ko gafakarsa,bazai shafa da hannunsa ba ko da sanda da wanin wannan, sai dai juzu'in Al-Qur'ani wanda ake koyon karatu dashi, ba zai shafa allon da aka rubuta Alkur'ani mai qirma a cikinsa ba, ba tare da alwala ba, sai dai wanda yake koyon karatu a cikinsa ko mai koyarwa wanda zai gyarashi (wato allon). Yaro karami kamar babba yake a hukuncin daukar Alkur'ani ko shafa shi, zunubi yana kan wanda ya baiwa yaro Alkur'ani mai girma. Wanda duk yayi salla ba tare da alwala ba, da gangan yana sane da zama kafiri (in dai ya halatta yin hakan) ALLAH S.W.T  ya tsare mu ameen. Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W 

DAREN FARKO (ABUNDA YA KAMATA SABBIN MA'AURATA SUYI A SHARI'ANCE)

1. Nafarko su fara da gaisuwa irin wadda addinin muslunci ya tanadar mana (watau suyi wa junan su sallama). 2. Sai ango ya daura hannunsa a bisa goshin amaryarsa ya karanta wannan addu'ar: "Allahumma innee as'aluka min khairiha wa khairi maa jabaltaha 'alaihi wa'a uzhubika min sharriha wa sharri maa jabaltaha 'alaihi" ( Abu Dawud Ibn Maajah Al-Haakim Al-Bahaki da Abu ya'ala). 3. Daga nan sai ango da amarya su gabatar da Alwala sannan su gabatar da Sallah raka'a biyu bayan sun idar sai su karanta addu'o'i na neman 'ya'ya na gari.

ABUBUWAN DAKE WARWARE ALWALA

Abubuwan da suke warware alwala sune kari da sabanin kari. Kari shine: fitsari da gyangyadi da rihi da maziyyi da wadiyyi. Sabanin kari sune: bacci mai nauyi da suma da maye da hauka da sumbata da shafar mace idan anyi niyyar jin dadi ko an samu jin dadin da shafar azzakari da cin tafin hannu ko cin yatsu. Hukuncin kari. Wanda yayi kokwanto a cikin kari ya wajaba a kansa ya sake alwala, sai dai idan ya kasance mai yawan kokwanto ne to babu komai a kansa. Ya wajaba a kansa ya wanke azzakarinsa gaba daya idan mazziyi ya fito, amman bazai wanke maraina ba. Note: mazziyi ruwa ne mai fitowa yayin karamar sha'awa ta hanyar tunani ko kallo ko waninsa. Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W