15 Jan 2017

KA KO SAN DA WANNAN A MUSULUNCI?

HADISI NA FARKO:

MANZON ALLAH (S.A.W) ya na cewa Wanda ya karanta Qulhuwallahu Ahad kafa 10x ALLAH ya yi masa Alkawarin zai gina masa katafaren gida a gidan Aljanna. Sai Sayyidina Umar ya ce Ai to in haka ne sai mu dinga yawaitawa, sai MANZON ALLAH (S.A.W) ya ce ALLAH (S.W.T) shine mai yawaitawa ALLAH (S.W.T) shine mai tsabtacewa. 


HADISI NA BIYU :

MANZON ALLAH (S.A.W) ya na cewa duk wanda ya karanta suratul Kahfi a ranar juma'a ALLAH (S.W.T) zai cika masa hasken sa har zuwa wata juma'a mai zuwa yana cikin haske yana cikin farin ciki.


HADISI NA UKU:

ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) ya ce duk wanda ya haddace ayoyin goma na farkon kahfi ALLAH (S.W.T) zai kiyaye shi daga fitinar Dujjal. 


HADISI NA HUDU:

MANZON ALLAH (S.A.W) yana cewa Wanda ya karanta ayatul kursiyu bayan kowace Sallah ta farillah ba abinda zai hana shi shiga Aljanna sai in bai mutu ba. 


HADISI NA BIYAR:

Idan kazo zaka kwanta a shimfidar ka moraddare to ka karanta kulya ayyu hal kafirun to bazaka mutu mushriki ba idan ka mutu a wannan daren. 


HADISI NA SHIDA:
 
Wanda ya yi alwala, bayan ya kare alwala sai ya ce Ash-hadu alla ilAha illallAh wahadahu lasharika lahu wa anna MUHAMMADAN Abduhu wara suluhu. Allahumma Ja'alni minattauwabina waja'alni minal mutadhahhirina. 
Duk wanda ya fadi wannan bayan gama Alwalar sa to za'a bude masa kofofin Aljanna guda takwas ya zabi wadda ya ke son shiga. 


HADISI NA BAKWAI:

Wanda ya yi alwala bayan ya kammala alwalar sa kaf, sai ya ce Subhanakallahumma Wabihamdika ash-hadu allah Ilaha illallah anta astagfiruka wa'atubu ilaika. 
Zaa rubuta wannan acikin wata takarda baza'a bude ta ba sai ranar lahira ya ga alkhairin da ke cikin ta. 


HADISI NA TAKWAS:

Wani Sahabi ya ke cewa wata rana muna tare da MANZON ALLAH (S.A.W) sai wani mutum daga cikin sahabbai ya ce Allahu Akbar kabirah, Walhamdulillahi kasirah, Wasubhanallahi bukratan waasilah, Sai MANZON ALLAH (S.A.W) ya ce wanene cikin ku ke fadar wannan kalma, sai ya ce ni ne Ya Rasulallah sai MANZON ALLAH (S.A.W) ya ce nayi mamakin wadan nan kalmomi da ka fada, anbude kofofin sama gaba daya saboda wannan kalma da ka fada.  Sai Abdullahi Dan Umar R.T.A ya ce tun daga wannan rana kullum sai na fadi wannan kalma, ban taba tsallake wata rana ko wani lokaci da bana fadar wannan kalma ba. 


HADISI NA TARA:

Wata rana mun kasance muna Sallah a bayan MANZON ALLAH (S.A.W) da Annabi ya dakko daga ruku'u sai ya ce Sami'Allahu Liman Hamidahu sai wani mutum daga cikin sahabbai yace Rabbana Walakal Hamdu, Hamdan Kasiran Dayyiban Mubarakan Fihi da aka gama sai MANZON ALLAH (S.A.W) ya waiwayo sai ya ce Wanene ya fadi wannan sai mutumin yace Ni ne ya MANZON ALLAH (S.A.W) sai MANZON ALLAH (S.A.W) ya ce Naga Malaika talatin da "yan kai suna rigagato wazai rubuta wannan aiki yaje ya gayawa ALLAH (S.W.T). 


HADISI NA GOMA:

MANZON ALLAH (S.A.W) ya ce Wanda ya yi sallar nafila raka'a goma sha biyu tsakanin dare da rana ALLAH (S.W.T) zai gina masa gida a cikin gidan Aljanna.


Salati ga SHUGABA S.A.W


madinatulahbab.blogspot.com Don ire iren sa

No comments:

Post a Comment