13 Oct 2016

BANBANCI TSAKANIN MANIYYI, MAZIYYI, WADIYYI, DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCEN SU

Wajibine kowani baligi ko baliga su san hukunce-hukuncen su domin gyara ibadunsu.

HUKUNCIN FITAR MANIYYI shine: fitowar sa tana wajabta wankan janaba akan namiji ko mace.

LAUNIN MANIYYIN NAMIJI: ruwane mai kauri fari wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da zakari. Sannan yana tunkudo juna lokacin dayake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari, idan ya bushe yana kamshin kwai.

LAUNIN MANIYYIN MACE: Ruwane tsinkakke, mai fatsi-fatsi, Wani lokacin kuma yana zuwa fari, wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji. Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa. Kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko damammen gari, idan ya bushe shima yana kamshin kwai.

HUKUNCINFITAR MAZIYYI: hukuncin sa shine a wanke farji gaba daya, da kuma inda ya shafa, kuma a sake alwala.

LAUNIN MAZIYYI: Ruwane tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar sha'awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce kakeso, ko matarka, ko kallon matar ko namijin da kike sha'awa. Haka kuma yana fitowa yayin wasa tsakanin miji da mata, saidai shi baya tafiyarda sha'awa, kuma wani lokacin ba'a sanin yafito.

Malamai suna cewa, Maziyyi yafi fitowa mata, fiye da maza.

HUKUNCIN WADIYYI: wadiyyi yana daukar hukunce-hukuncen fitsari ne.

WADIYYI: Wani ruwane mai kauri dayake fitowa a karshen fitsari, ko kuma karshen bahaya ga wanda ya jima bai yiba, yana fitowa ga wadanda ba suda aure, ko wadanda suka yi nisa da abokin
rayuwarsu ta aure, ina nufin namiji ko mace.

Amman fa ku sani komai saida niyya

ALLAH S.W.T shine mafi sani!!!

No comments:

Post a Comment