Skip to main content

Posts

Showing posts from October, 2016

BANBANCI TSAKANIN MANIYYI, MAZIYYI, WADIYYI, DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCEN SU

Wajibine kowani baligi ko baliga su san hukunce-hukuncen su domin gyara ibadunsu. HUKUNCIN FITAR MANIYYI shine: fitowar sa tana wajabta wankan janaba akan namiji ko mace. LAUNIN MANIYYIN NAMIJI: ruwane mai kauri fari wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da zakari. Sannan yana tunkudo juna lokacin dayake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari, idan ya bushe yana kamshin kwai. LAUNIN MANIYYIN MACE: Ruwane tsinkakke, mai fatsi-fatsi, Wani lokacin kuma yana zuwa fari, wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji. Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa. Kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko damammen gari, idan ya bushe shima yana kamshin kwai. HUKUNCINFITAR MAZIYYI: hukuncin sa shine a wanke farji gaba daya, da kuma inda ya shafa, kuma a sake alwala. LAUNIN MAZIYYI: Ruwane tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar sha'awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce kakeso, ko matark

MAGANIN MATSALOLI 7

Mutumin da yake cikin tsoro ya lazumci karanta: HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL. Mutumin da bakin ciki ya dame shi ya lazumci karanta: LA ILAHA ILLA ANTA SUB'HANAKA INNEE KUNTU MINAZ ZALIMEENA. Mutumin da masu makirci suka dame shi da makirci ya lazumci karanta: WA UFAWWIDHU AMREE ILAL LAAH. INNAL LAAHA BASEERUN BIL 'IBAADI. Mutumin da yake fama da wata jinya ko rashin lafiya, ya yawaita karanta: RABBI ANNEE MASSANIYADH DHURRU WA ANTA ARHAMUR RAHIMEENA.