5 Jan 2016

WANKAN JANABA (FARILLAI, SUNNONI DA MUSTAHABI) DA HUKUNCI A CIKIN WANKAN

FARILLAN WANKA: Yin niyya yayin farawa da gaggautawa da cuccudawa da gama jiki da ruwa.

SUNNONIN WANKA: Wanke hannaye ya zuwa tsintsiyar hannu kamar yadda akeyi a alwala, da kurkure baki, da shaka ruwa, da fyacewa, da wanke kofar kunnuwa itace kofa mai shiga cikin kai, amman fatar kunne wajibine a wanke cikinta da bayanta.

MU SAHABBAN WANKA: Farawa da wanke najasa, sannan a wanke azzakari inda a nan ne zaiyi niyyar wankan, sannan ya wanke gabban alwala sau dai-dai, sannan ya wanke saman jikinsa, da wanke kai sau uku da gabatar da tsagin jikinsa na dama, da karanta ruwa akan gabbai.


HUKUNCE HUKUNCEN WANKA


wanda ya manta wani gurbi da bai sami ruwa ba, ko gaba guda a wankansa, to yayi maza ya wanke su da zarar ya tuna koda bayan wata guda ne da yin wankan, sannan ya sake duk sallolin da yayi kafin wankewar, idan ya jinkirta wankewar bayan tuwarsa to wankan nasa ya baci.

Idan a cikin gabban alwala ne kuma ya zamana ya riga ya wanke shi a cikin alwalar wankan to wannan ya wadatar.

Shiga masallaci  bai halatta ba ga mai janaba, da karatun Alkur'ani sai dai aya daya ko makamanciyar ta, don neman tsarin kai da makamancin sa.

Bai halatta ga mutumin da bazai iya taba ruwa ba, ya sadu da iyalinsa har sai ya tanadi abin dafa ruwa, sai dai idan mafarki yayi, to wannan babu komai a kansa.
ALLAH S.W.T ne masani.

Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W 

No comments:

Post a Comment