5 Jan 2016

RANAKU DA LOKUTTAN DA ANSO A GABATAR DA JIMA'I A CIKINSU

Ranaku da aka so ango ya gabatar da jima'i  da amaryarsa, domin fa'ida da samun falalarsu.

Daren litinin, ana samun mahaddacin Alkur'ani.

Daren talata, ana samun yaro/yarinya Shahidi.

Daren alhamis, ana samu yaro/yarinya mai yawan tsoron ALLAH S.W.T, ko kuma wayayye mai kwarjini.

Ranar juma'a kafin a tafi sallar Juma'a,  ana samun yaro/yarinya mai sa'a tare da samun kyakkyawan karshe.

Jima'i a daren Juma'a na da matukar kyau domin shine mafi darajar darare guda bakwai.
Annabi S.A.W yace:


"yanxu dayanku sai ya gaji da yin jima'i da iyalinsa ranar Juma'a? Hakika yana da ladan wankansa da ladan wankan matarsa."(Baihaki ne ya ruwaito)


Lokutan da aka so ango ya gabatar da jima'i da amaryarsa

Ana bukatar ango yayi jima'i da amaryarsa a lokacin da take cikin farin ciki da annashuwa, malamai masana ilimin jima'i  sunyi hani ga ango da amarya ko maigida da uwargida su gabatar da jima'i a cikin wani hali na rashin kwanciyar hankali, ko kuma a lokacin da ango da amarya suke jin yunwa, kishir-ruwa, halin bacin rai, ko kuma rashin lafiya.

Sannan an samo a cikin littafin DIBBUN NABAWI, cewa kyakkyawan lokacin gabatar da jima'i shine a lokacin da dare ya taho qarewa, domin a farkon dare ciki cike yake da abinci. Kuma akwai karancin sha'awar jima'i in ango ya koshi sosai.

Nana Aisha R.T.A ta ruwaito cewa:

"Yana daga kyakkyawar dabi'ar Manzon Allah S.A.W  bayan ya kammala sallar nafila a tsakiyar dare ya kan sadu da iyalinsa in yana da bukata, in kuma bashi da bukata sai ya kwanta akan abin sallar sa har sai Bilal R.A ya kira asuba."

Ku sani cewar Shari'a bata haramta aiwatar da jima'i a farkon dare ba, sai dai malamai masana ilimin jima'i sun fitar da bayanin cewa a karshen dare yafi saboda samar da lafiya da kare kai daga wadansu cututtuka.

Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W 

5 comments: