4 Jan 2016

NIYYAR GABATAR DA JIMA'I

GABATAR DA ADDU'O'I KAFIN JIMA'I

Domin neman tsari daga shaidanu da kuma wasu illoli, anso lokacin da ango ke jima'i da amaryarsa ya karanta wannan addu'o'i,  ta wannan hanya ango da amarya zasu samu tsari.

"Bismillahi Allahumma jannibnash shaidana wa jannibish shaidana ma razaktana"

A lokacin da ango zai inzali (wato zai kawo maniyyi) zai karanta wannan addu'ar

"Allahumma lataja alli shaidana fiimaa razaktana nasiiba."

Wadannan  addu'o'i na da matukar Muhimmanci ga ango da amarya, don haka nake kira ga sabon ango yayi kokarin haddace wadannan addu'o'i kuma yayi kokarin koyawa amaryar in har bata iya ba.


Kuma su rika kokarin karantawa a lokacin da aka bukata su karanta.

"A lokacin gabatar da jima'i, ya kamata ango ya daura wadannan niyyoyi"

1. Ango ya daura niyyar kare kansa daga zina.

2. Da niyyar kare kansa daga kallon matan da ba halal din sa ba.

3. Da niyyar samar da 'ya'ya na gari wadanda zasu yiwa Musulunci hidima. In har ango ya gabatar da jima'i  da amaryarsa tare da kyakkyawar niyya ya sami gamsuwa da ita akwai lada da ALLAH Madaukakin Sarki zai bashi.

Wannan na nuni ne da Muhimmancin sanya kyakkyawar niyya a zukata kafin saduwar jima'i, kuma ana samun falala daga wannan niyyoyi kyawawa.

Anso a lokacin da ango da amarya ke shirin saduwa su tube tufafinsu, sannan su lullube a cikin mayafi kada suyi jima'i tsirara. Bayan sun lulluba, su kashe fitila.

ALLAH S.W.T ne masani.

Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W

No comments:

Post a Comment