19 Jan 2016

LOKUTTAN DA ANSO KADA A GABATAR DA JIMA'I

Makaruhi ne ango da amarya ko maigida da uwargida su gabatar da jima'i a cikin darare ukku na kowane wata, wadannan darare kuwa sune:
1. Daren farkon kowane wata.
2. Daren karshen wata.
3. Daren tsakiyar wata.Shaidan yana yawo a cikin wadannan darare, rashin son a gabatar da jima'i a wadannan darare ya fito ne daga su Abu Huraira (R.A).

Bayan haka marubucin littafin 'RIFATUL MUSLIMIN' ya fadi cewa:
1. Daren laraba
2. Daren babbar Sallah
3. Daren karamar Sallah

Na daya daga cikin dararen da anso kada maigida ko ango ya gabatar da jima'i da matarsa. Sannan akwai daren da maigida ya daura niyyar tafiya washe gari, Shima anso kada a gabatar da jima'i a cikinsa. Jima'i a cikin wadannan darera na iya haifar da wasu manyan matsaloli ga Dan.

ALLAH S.W.T ne masani
Salati 10 ga Annabi Muhammad S.A.W

2 comments: