20 Jan 2016

HUKUNCIN YAWAN KOKONTO A CIKIN SALLAH

mai yawan shakku shine yayi kokari wajan yin sallah cikin jama'a wato tare da liman, Idan haka bata samuba sai ya lura da kokonton Nasa dadine ko ragi Idan ragine sai yazo da abunda ya rage sai yayi sujjada ba'adi, Idan karine sai yayi sujjada ba'adassalami shima.

Kasani/kisani cewa mai mantuwa kashi Uku ne.

1- Wanda ya manta ko ya kara cikin wani Abu na farillah.

Wannan dole sai yazo da Abunda ya rage Idan yakai matsayin farillah dole sai yacikoshi sai yayi sujja bayan sallama Idan ya bai tunaba har saida ya sallame Kuma Aka samu lokaci sallar ta baci sai ya sake Idan kuma ya tuna a kusa sai ya kawo Abunda ya rage yayi sujjada bayan sallama.


2- Shine Wanda ya rage Sunnoni biyu shi basai ya cikoba zaiyi sujjada kafin sallam ne Idan ya manta haryai sallama sai yayi sujjada bayan sallama.

3- Shine Wanda ya rage wani Abu daga cikin mustahabi babu sujjada gareshi  Idan kuma yayi sujja kably dan ya rage Mustahabi to sallar ta baci.

Idan kuma shakkun nasa cikin Alwala ne yake yawan kamashi toh. Kawai yayi sallah da alwalar koda yana shakkun saidai bazai yiwu yayi sallah biyu da itaba.
ALLAH S.W.T ne masani.
Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W

No comments:

Post a Comment