3 Jan 2016

ABUBUWAN DA AKA HARAMTA MARA ALWALA YI

Salla, tawafi, shafar Al-Qur'ani mai girma ko gafakarsa,bazai shafa da hannunsa ba ko da sanda da wanin wannan, sai dai juzu'in Al-Qur'ani wanda ake koyon karatu dashi, ba zai shafa allon da aka rubuta Alkur'ani mai qirma a cikinsa ba, ba tare da alwala ba, sai dai wanda yake koyon karatu a cikinsa ko mai koyarwa wanda zai gyarashi (wato allon).

Yaro karami kamar babba yake a hukuncin daukar Alkur'ani ko shafa shi, zunubi yana kan wanda ya baiwa yaro Alkur'ani mai girma.

Wanda duk yayi salla ba tare da alwala ba, da gangan yana sane da zama kafiri (in dai ya halatta yin hakan) ALLAH S.W.T  ya tsare mu ameen.

Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W 

No comments:

Post a Comment