8 Nov 2015

YADDA AKEYIN SALLAR GAWA

Yanda Akeyin Sallar gawa daga Annabi (saw).

Kamar yanda wasu daga cikin 'yan uwa  Suka nema cewa Ayiwa mutane Karin bayani Akan Sallar Jana'iza Muna Rokon Allah ya bamu dacewa cikin Abunda zamu fada.

Da farko dai mutum Zai Qudurta Niyya a ransa.
Idan Namiji ne mamacin Sai liman ya tsaya saitin kan sa, Idan Mace ce Sai liman ya tsaya tsakiyar ta daidai.
Sai yayi kabbara ta farko, sai Fathi daya da sura cikin gajerun Surori ko wasu Ayoyi a takaice Sai ya sake Kabbara ta biyu, sai ya kawo Salati ga Annabi (saw) Salatu Ibrahimiyya. Sai yayi kabbara ta Uku, bayan kabbara ta Uku sai ya kawo wannan Adu'ar

(ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﺤﻴﻨﺎ ﻭﻣﻴﺘﻨﺎ ﻭﺷﺎﻫﺪﻧﺎ ﻭﻏﺎﺋﺒﻨﺎ ﻭﺻﻐﻴﺮﻧﺎ ﻭﻛﺒﻴﺮﻧﺎ ﻭﺫﻛﺮﻧﺎ ﻭﺃﻧﺜﺎﻧﺎ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻣﻦ ﺃﺣﻴﻴﺘﻪ ﻣﻨﺎ ﻓﺄﺣﻴﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻹﺳﻼﻡ، ﻭﻣﻦ ﺗﻮﻓﻴﺘﻪ ﻣﻨﺎ ﻓﺘﻮﻓﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻪ ﻭﺍﺭﺣﻤﻪ ﻭﻋﺎﻓﻪ ﻭﺍﻋﻒ ﻋﻨﻪ، ﻭﺃﻛﺮﻡ ﻧﺰﻟﻪ ﻭﻭﺳﻊ ﻣﺪﺧﻠﻪ، ﻭﺍﻏﺴﻠﻪ ﺑﺎﻟﻤﺎﺀ ﻭﺍﻟﺜﻠﺞ ﻭﺍﻟﺒﺮﺩ، ﻭﻧﻘﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﺨﻄﺎﻳﺎ ﻛﻤﺎ ﻳﻨﻘﻰ ﺍﻟﺜﻮﺏ ﺍﻷﺑﻴﺾ ﻣﻦ ﺍﻟﺪﻧﺲ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﺑﺪﻟﻪ ﺩﺍﺭﺍً ﺧﻴﺮﺍً ﻣﻦ ﺩﺍﺭﻩ، ﻭﺃﻫﻼ ﺧﻴﺮﺍً ﻣﻦ ﺃﻫﻠﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﺩﺧﻠﻪ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻭﺃﻋﺬﻩ ﻣﻦ ﻋﺬﺍﺏ ﺍﻟﻘﺒﺮ ﻭﻣﻦ ﻋﺬﺍﺏﺍﻟﻨﺎﺭ، ﻭﺍﻓﺴﺢ ﻟﻪ ﻓﻲ ﻗﺒﺮﻩ ﻭﻧﻮﺭ ﻟﻪ ﻓﻴﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ
ﺗﺤﺮﻣﻨﺎ ﺃﺟﺮﻩ ﻭﻻ ﺗﻀﻠﻨﺎ ﺑﻌﺪﻩ)

Idan macece sai ya canza lamirin Hi Hi Hi Hi Hi Zuwa Ha Ha Ha Ha Ha. Sai yayi kabbara ta Hudu, bayan kabbara ta Hudu Sai ya dan saurara Kadan sai yayi Sallama daya Gefen damar sa.

Ya Allah kasa mucika da Imani Dan Alfarmar Annabi Muhammadu (saw).

source: Malam Abdulhadi Gashu'a.