9 Nov 2015

FASALI A CIKIN BAYANIN TSARKI (RABE-RABEN TSARKI)TSARKI YA KASU KASHI BIYU: Tsarkin kari da tsarkin dauda, gaba dayansu ba sa inganta sai da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa, shine wanda launinsa bai jirkita ba da basa haduwa da shi a bisa hali mafi yawa, kamar misalin narkakken mai da sandararren mai da romo gaba dayansu da shuni da sabulu da dauda da makamancinsu, babu laifi idan ya hadu da tulbaya da kasar kanwa da kasar gishiri da jar kasa da makamancinsu.

FASALI: idan najasa ta ayyana (wato aka san wurin da take) sai a wanke wurinta, idan ta rikitar sai a wanke tufan gaba dayansa
samuwar najasa sai ya yayyafa ruwa, idan wani abu ya same shi ya yi kokwanto a cikin najasarsa to babu yayyafi a kansa. Wanda ya tuna najasa yana cikin salla sai ya yanke sai dai in ya ji tsoron fitar lokaci, wanda ya yi salla da najasa yana mai mantawa, sai ya tuna bayan sallama to ya sake salla a cikin lokaci.

::ALLAH NE MASANI