6 Nov 2015

FARKON ABINDA YAKE WAJABA AKAN BALAGAGGE

Ya iganta imaninsa sannan yasan abinda zai kyautata farillan aininsa da shi, kamar ilimin hukunce-hukuncen sallah da tsarki da azumi.
Ya wajaba a kansa ya kiyaye iyakokin ALLAH tsarkakken Sarki tun baiyi azaba a gare shi ba.
Ya wajaba a kansa ya kiyaye harshensa daga maganganu na sabo da munanan maganganu da duk wani zance mara dadi, ya kiyaye harshensa daga rantsuwa da sakuwar matsarsa, ya nisanci yin barazana ga musulmi da walakantashi, da zaginsa da tsorata shi ba tare da hakkin shari’a ba.
Ya wajaba a kansa ya kiyaye ganinsa daga kallon haramun, bai halatta ba a gare shi ya kalli musulmi da irin kallon da zai cuce shi, sai dai idan musulmin mai yawan sabo ne a fili, toh wannan ya zama dole ya kaurace masa.
Ya wajaba a kansa ya kiyaye dukkanin gabbansa iyakar ikonsa. Ya yi soyayya don ALLAH, ya yi kiyayya don ALLAH, ya yarda da mutum saboda ALLAH, ya yi fushi don ALLAH, ya rika yin umarni da kyawawan aiki, ya yi hani ga barin mummunan aiki.
Karya ta haramta a gare shi, da giba, da annamimanci, da girman kai da kaye, da riya, da jiyarwa, da hassada, da gaba, da ganin fifiko akan wani, da yafice, da zunde, da wasa, da izgili, da zina, da kallon mace ajnabiyya, da jin dadin firarta, da cin dukiyar mutane ba tare da dadin rai ba, da ci da sunan ceto ko da sunan addini, da jinkirta sallah ga barin lokutanta.
Bai halatta a gare shi ba yayi abota da fasiki, ko ya zauna da shi in dai bada lalura ba, kada ya nemi yardar halatta a cikin abinda zai sabawa ALLAH Mahalicci.
ALLAH mai tsarki da daukaka ya ce : ( ALLAH da MANZONSA su ne suka fi wajaba mutane su nemi yardarsu indai sun kasance masu imani ) Suratul-Tauba 621.
Mai tsira da amincin ALLAH ya ce: “babu biyayya ga wani abin halitta a cikin sabon mahalacci”
Bai halatta ba a gare shi ya yi wani aiki har sai ya san hukuncin ALLAH a cikinsa, (idan bai sani ba) ya tambayi malamai, ya yi koya da masu bin Sunnar ANNABI MUHAMMADU (S.A.W), wadanda suke shiryawa ga bin ALLAH TA’ALA, masu tsoratawa ga barin bin shaidan, kada ya yardarwa kansa irin abinda ababan fallasa suka yarda dashi, wadanda rayuwarsu ta tozarta a cikin bin wanin ALLAH TA’ALA, ya girman asarar irin wadannan mutane, ya tsawan kukansu ranar Alkiyama”.
Muna rokon ALLAH yayi mana mawafaka ga bin Sunnar ANNABINMU MACECINMU SHUGABANMU MUHAMMADU S.A.W.s