Skip to main content

Posts

Showing posts from November, 2015

FASALI A CIKIN BAYANIN TSARKI (RABE-RABEN TSARKI)

TSARKI YA KASU KASHI BIYU: Tsarkin kari da tsarkin dauda, gaba dayansu ba sa inganta sai da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa, shine wanda launinsa bai jirkita ba da basa haduwa da shi a bisa hali mafi yawa, kamar misalin narkakken mai da sandararren mai da romo gaba dayansu da shuni da sabulu da dauda da makamancinsu, babu laifi idan ya hadu da tulbaya da kasar kanwa da kasar gishiri da jar kasa da makamancinsu. FASALI: idan najasa ta ayyana (wato aka san wurin da take) sai a wanke wurinta, idan ta rikitar sai a wanke tufan gaba dayansa

FARILLAN ALWALA, SUNNONIN ALWALA, MUSTAHABBAN ALWALA DA KUMA YADDA AKE GYARA ALWALA

F arilla alwala: niyya da wanke fuska da wanke hannaye zuwa gwiwar hannu da shafar kai da wanke kafafuwa zuwa ido-sawu da cucudawa da gaggautawa. Sunnonin alwala: wanke hannaye izuwa tsintsiyar hannu yayin farawa, da kurkure baki, da shaka ruwa, da fyacewa, da dawo da shafar kai, da shafar kunnuwa, da sabunta ruwa dan shafar kunnuwa, da jeranta farillai.

YADDA AKEYIN SALLAR GAWA

Yanda Akeyin Sallar gawa daga Annabi (saw). Kamar yanda wasu daga cikin 'yan uwa  Suka nema cewa Ayiwa mutane Karin bayani Akan Sallar Jana'iza Muna Rokon Allah ya bamu dacewa cikin Abunda zamu fada. Da farko dai mutum Zai Qudurta Niyya a ransa. Idan Namiji ne mamacin Sai liman ya tsaya saitin kan sa, Idan Mace ce Sai liman ya tsaya tsakiyar ta daidai. Sai yayi kabbara ta farko, sai Fathi daya da sura cikin gajerun Surori ko wasu Ayoyi a takaice Sai ya sake Kabbara ta biyu, sai ya kawo Salati ga Annabi (saw) Salatu Ibrahimiyya. Sai yayi kabbara ta Uku, bayan kabbara ta Uku sai ya kawo wannan Adu'ar

SHARUDDAN TUBA

Yin nadama akan abinda ya wuce, da yin niyyar ba za a sake komawa kan sabon ba har abada. Kuma ya bar sabon nan-take idan ya kasance yana cikin aikin sabon ne. bai halatta a gare shi ba ya jinkirta tuba, bai halatta ba ya ce; in ALLAH ya shirye ni na tuba ba, fadar haka yana daga alamomin rashin arzikin lahira da tabewa da rashin basira.

FARKON ABINDA YAKE WAJABA AKAN BALAGAGGE

Ya iganta imaninsa sannan yasan abinda zai kyautata farillan aininsa da shi, kamar ilimin hukunce-hukuncen sallah da tsarki da azumi. Ya wajaba a kansa ya kiyaye iyakokin ALLAH tsarkakken Sarki tun baiyi azaba a gare shi ba. Ya wajaba a kansa ya kiyaye harshensa daga maganganu na sabo da munanan maganganu da duk wani zance mara dadi, ya kiyaye harshensa daga rantsuwa da sakuwar matsarsa, ya nisanci yin barazana ga musulmi da walakantashi, da zaginsa da tsorata shi ba tare da hakkin shari’a ba.