30 Oct 2015

ISTIMNA'I (masturbation) da HUKUNCIN SA

ISTIMNA'I ( masturbation)

shine shine mutum ya rika wasa da al'aurassa har ya fitar da maniyyi,

HUKUNCIN ISTIMNA'I

Farko dai akwai hadisai wadanda suka nuna fushi na ubangiji akan mai aikata hakan,
Hukuncinsa ga malaman mazhabobi guda hudu,

Imam Malik Imam Shafi'i.
Sun tafi akan haramta shi don haka a wurin su dole mutum yayi aure ko ya kame har zuwa lokacin da Allah zai bashi ikon yin aure.


Imam Abu hanifa.
Shi kuma ya tafi akan halas ne amma da sharadi, sharadin kuwa shine Sai in sha'awa ta tasoma mutum kuma sha'awar tazo ne kurum daga Allah ba wai mutum da kansa bane ya kirkiri hanyar zuwan sha'awar da kansa ba. To anan Imma abi haneefa yace halas ne mutum yayi ISTIMNA'I.

Imam Ahmad bin hanbal.
Shi kuma ya tafi akan cewa halas ne kuma babu wani sharadi don haka a gunsa ya halatta ka iya kirkiro sha'awar da kanka kuma kaji dadi ta hanyar istimna'i. Hujjarsa itace da mutum yayi zina dama yayi hakan.

Wannan shine abunda na dan sani akan istimna'i Sannan ka sani fa su kansu wadanda suka halasta suna magana ne akan wadanda Allah bai ba ikon abunda zai aure ba Wannan abunda ya shafi hukuncinsa a addini kenan .
Sannan game da lafiyar jiki mutane na maganganu da yawa akan cewa yana sa ramar jiki yana kuma haddasa raunin idanu har ya zuwa makanta yana kuma haddasa yawan mantuwa da dai sauransu.