23 Dec 2014

ADDUAR DA MANZON ALLAH (SAWW) YAKE KARANTAWA IDAN ZAI KWANTA BARCI

ﺑِﺎﺳْﻤِﻚَ ﺭَﺑِّﻲ ﻭَﺿَﻌْﺖُ ﺟَﻨْﺒِﻲ، ﻭَﺑِﻚَ ﺃَﺭْﻓَﻌُﻪُ، ﻓَﺈِﻥْ ﺃَﻣْﺴَﻜْﺖَ ﻧَﻔْﺴِﻲ ﻓَﺎﺭْﺣَﻤْﻬَﺎ، ﻭَﺇِﻥْ ﺃَﺭْﺳَﻠْﺘَﻬَﺎ ﻓَﺎﺣْﻔَﻈْﻬَﺎ، ﺑِﻤَﺎ
ﺗَﺤْﻔَﻆُ ﺑِﻪِ ﻋِﺒَﺎﺩَﻙَ ﺍﻟﺼَّﺎﻟِﺤِﻴﻦَ .
Bismika Rabbee wadha'atu janbee , wa bika 'arfa'uhu, fa'in 'amsakta nafsee
farhamhaa, wa 'in 'arsaltahaa fahfaz'haa, bimaa tahfazu bihi 'ibaadakas-saal
iheen.

MA'ANA : Da albarkar sunanka ne Ya Allah nake Kwantar da hakarkari na, Kuma da albarkar Sunanka ne zan tasheshi. Idan zaka karbi raina ne (acikin daren nan) to Ya Allah ka jikanta. Idan kuma zaka saki (rai na ne) To (Ya Allah ) ka kiyayeta da irin abinda kake kiyaye bayinka nagartartu. Idan kuma ka farka kaje bawali ka dawo, to anaso ka karkade shimfidar sannan kace BISMILLAHI kafin ka kwanta. Domin kuwa baka sani ba, ko wani abin ya maye gurbinka alokacin da ka fita.

Salati 10 ga Annabi S.A.W