18 Nov 2014

FAIDODIN SALATUN NABIYYI (SAWW)

Idan ka yawaita salati da tasleemi ga Manzon Allah (saww) zaka samu rabauta da
fa'idodi Masu yawa Kamar haka:

1. Cika Umurnin Allah da yace: "Salluu 'alaihi wa
sallimuu tasleeman".

2. Allah zai maka salatai guda 10 IRIN NASA (SWT).

3. Allah zai sa Mala'ikinsa ma suyi maka salati.

4. Zaka samu biyan bukatarka da gaggawa, domin kuwa Salatun Nabiyyi (saww)
shine mabudin kofar samun karbuwar Addu'a.5. Zaka damu gafarar Zunubanka.

6. Zaka samu yayewar Bakin-cikinka. Ko yanzu idan kana da damuwa, da zarar
kayi salati zakaji farin ciki. Bakin cikinka ya yaye.

7. Wajen zamanka zai rika Kamshi. (Mala'iku suna jin Qamshi yana tashi daga
duk guraren da ake yin Salati ga Manzon Allah (saww).

8. Zaka samu QARUWAR SOYAYYARSA (SAWW)
ACIKIN ZUCIYARKA.

9. Allah (swt) zai So ka. Soyayya ta musamman.

10. Zaka samu Qaruwar shiriya.

11. Zuciyarka ba zata mutu ba, albarkacin hasken wannan salatin.
12. ZAKA SAMU QARIN KUSANCI DASHI (SAWW).

13. Zaka fita daga cikin layin marowata awajen Allah.

14. Kaima Allah zai ambaceka acikin Mala'ikunsa.

15. Zaka samu hasken fuska aranar Alqiyamah.

16. Zaka samu zama tare da Manzon Allah (saww) aranar Alqiyamah.

17. Samun cetonsa mai girma, da kuma shiga Aljannah tare dashi (saww).

18. Zaka samu karbuwar ibadunka.

YA ALLAH KAYI SALATI MAFI GIRMA ABISA MAFI GIRMA AWAJENKA ANNABINMU
MUHAMMADU S.A.W DA IYALAN GIDANSA DA DUKKAN SAHABBANSA DA MASOYANSA DA SALIHAN BAYINKA.

Salati 10 ga Annabi S.A.W