Skip to main content

Posts

Showing posts from November, 2014

ISTIGFARIN DAYA FI KOWANE ISTIGFARI

Allahumma anta rabbi lailahailla anta kalaqtani, wa ana abduka wa ana ala ahadika wawa'adika mastada'atu auzubika min sharri maa sana'atu, abu'ulaka bi ni'imatika alaiya wa abu'ubizambi fagfirli fa innahu layagafiru zunuba illa anta. wanda duk ya fadeta da rana yana mai yakini da ita sai ya mutu a wannan yinin wannan yana daga ahlin aljanna. wanda ya karanta da dare shima da yakini akanta shima dan aljanna ne. Salati 10 ga Annabi S.A.W 

SALATUL ISTIHARA

MANZON ALLAH mai tsira da amincin ALLAH ya kasance yana sanar damu yanda ake istihara acikin kowane irin al'amurra da muka kasance, harma yake cewa 'duk lokacin da daya daga cikinku ya kasance mai himmatuwa ya zuwa wani aiki to sai yai sallah raka'a biyu (2) sannan sai yace  "ALLAHUMMA INNI ASTAKIRUKA BI ILMIKA WA'ASTAQADIRUKA BI QUDIRATIKA WA'AS'ALUKA MIN FADALUKAL AZIM FA INNAKA TAQDIRU WALA AQDIRU Fa AnTA taALAMU WALA A'ALAMU WA'ANTA ALLAMULGUYUB, ALLAHUMMA IN KUNTA TA'ALAMU ANNA HAZAL AMRA KHAIRUNLI FIDINI WA MA'ASHII WA'AQIBATU AMRI"  Ko kuma mutum yace

FAIDODIN SALATUN NABIYYI (SAWW)

Idan ka yawaita salati da tasleemi ga Manzon Allah (saww) zaka samu rabauta da fa'idodi Masu yawa Kamar haka: 1. Cika Umurnin Allah da yace: "Salluu 'alaihi wa sallimuu tasleeman". 2. Allah zai maka salatai guda 10 IRIN NASA (SWT). 3. Allah zai sa Mala'ikinsa ma suyi maka salati. 4. Zaka samu biyan bukatarka da gaggawa, domin kuwa Salatun Nabiyyi (saww) shine mabudin kofar samun karbuwar Addu'a.

Sayyiduna Abubakrin R.A

Sayyiduna Abubakrin bai fifici sauran Sahabbai da yawan Sallah ko yawan Azumi, ko yawan Ruwayar Hadisai ba. Sai dai ya Fificesu ne da Yawan Soyayyar Manzon Allah (S.A.W.W). Wannan Soyayyar ta sanya ba ya ganin komai agabansa sai Allah da Manzonsa (S.A.W.W). Kuma wannan Soyayyar ce ta sanyashi yake da saurin Gaskatawa da zarar wani Umurni ko hani ya sauka. Wannan Soyayyar ce ta sanya Allah ya zabeshi ya zama Khalifan farko daga cikin Khalifofin Masoyinsa (S.A.W.W). Haka nan shima Manzon Allah (S.A.W.W) yana mutukar Qaunar Sayyiduna Abubakar (R.A). Har Watarana Sayyiduna Amru bn Al-aas (R.A) ya tambayi Manzon Allah (S.A.W.W) Wanene Wanda kafiso acikin Mutane baki dayansu?" Sai yace masa "A'isha". Sai yace "Acikin Maza fa?" Sai yace "Abubakar ne". Mutane sukan fuskanci bacin rai sosai daga Manzon Allah (S.A.W.W) aduk lokacin da suka 'bata ran Sayyiduna Abubakrin. Wannan Qarfin Soyayyar ce ta sanya Sayyiduna Abubakrin yafi kowa Imani

Dr Maqary yakan ce

"Yanzu alumman musulmi sun zama in dai suna son mutum  ko don kungiyansu daya ko aqeeda ko Wani dalili dai ya hada su tohm baya laifi a  wurrinsu duk ko girman laifin da yayi Zaa nemi uzuri... Idan yana iskanci ace  jazba ne. Idan asharari ne ace sahibul haal ne... Idan kuwa baa son shi tohm Abu  kadan Zai fada ko da ba hakan ya nufa ba a juya mashi magana ayi tawili ace ai  Ga abunda yake nufi ... Kuma ayi ta yayatawa..." Rab Sitteer ya rajul

CETON ANNABI GASKIYA NE

Shine farkon wanda zai nemi ceto awajen Ubangijinsa, kuma shine farkon wanda  za'a bama damar yayi ceto 1. Da farko zai ceci dukkan halitta, albarkacin ceton nasa (S.A.W.W) ne ma Ubangiji zai saurari halitta harma ayi musu hisabi 2. Akarkashin cetonsa (S.A.W.W) ne Sauran Annabawa da Manzanni suma zasuyi ceto abisa al'ummominsu 3. Waliyyan Allah, Shahidai da sauran Muminai su ma zasuyi ceto akarkashin cetonsa (S.A.W.W) 4. Zai ceci Ma'abota tarin Zunubi daga cikin al'ummarsa (S.A.W.W), Sanna daga Qarshe zaije har cikin Jahannama ya rika fidda Mutane. Ba zai bar duk wani Musulmi ko Mumini ba, sai ya fidda dukkan wanda yake da Imani azuciyarsa koda Misalin Kwayar Zarrah ne Ya Allah Domin falalarka da Rahamarka, Don Girman Jamalar Zatinka ka sanyamu acikin wadanda zasu shiga Aljannah ba tare da hisabi ko Uqubah ba.

ANNABI MUHAMMAD RASULULLAH (S.A.W.W) yace:

"waye zai karbi wadannan kalmomi guda biyar |5| yayi aiki dasu kuma yakarantar da mai aiki dasu? Sai Abu-Huraira yace gani nan, sai Annabi Muhammadu (s.a.w) yakama Abu-Huraira ya kirga yatsu biyar sai yace: 1:-Kakiyayi haramu, zaka kasance mafi Ibadan mutane. 2:-Kayarda da abinda Allah yabaka, zaka kasance mafi wadatar mutane. 3:-Ka kyauta tawa makabcinka, zaka kasance mumini. 4:-Kasowa mutane abinda kasowa kanka, zaka kasance musulmi. 5:-Kada kayawaita dariya, lalle yawa dariya tana kashe zuciya.Allah ya kiyayemu baki daya.Ameen Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W 

An Tambayi Manzon Allah (saww) Akan abubuwan da zasu shigar da Mutumgidan Aljannah. Sai yace:

An Tambayi Manzon Allah (saww) Akan abubuwan da zasu shigar da Mutum gidan Aljannah. Sai yace: "TSORON ALLAH, DA KUMA KYAWAWAN 'DABI'U". Sannan aka tambayeshi akan abubuwan da zasu sanya Mutum shiga Wuta, Sai yace: "HARSHE DA KUMA AL-AURA". - Imam Tirmizy ne ya ruwaito hadisin. Wannan hadisin yana karantar damu Muhimmancin kyawawan Dabi'u da kuma sanya Tsoron Allah azuciya, Sannan mutum ya guji fadar duk abinda yazo bakinsa, kuma mutum ya kiyaye Sha'awarsa. Ya Allah ka tsaremu da Qarfin Ikonka ameen. Salati 10 ga Annabi Muhammadu S.A.W