Skip to main content

DARAJOJI GUDA 10 GAME DA SAYYIDUNA UTHMAN BN AFFAN (rta)

DARAJOJI GUDA 10 GAME DA SAYYIDUNA UTHMAN BN AFFAN (rta)
Kafin mutuwar Shahadarsa, Sayyiduna Uthman (ra) ya gaya ma ABU THAWR AL-
FAHMIY cewa: "Ina Kyautata zato awajen Ubangijina saboda wasu abubuwa guda
goma wadanda na sanyasu amatsayin amana tsakanina dashi. Abubuwan sune:
1. Nine mutum na hudu wajen shiga Musulunci.
2. Manzon Allah (saww) ya aura min 'Yarsa ta cikinsa.
3. Da ta mutu ya Qara aura min da 'Yar uwarta.
4. Tunda nake ban ta'ba rera waka ba.
5. Tunda nake ban ta'ba Tunanin aikata mugunta ba.
6. Tun daga ranar da nayi mubaya'a ga Manzon Allah (saww) da hannuna na
dama, ban sake shafar al'aurata da wannan hannun ba.
7. Tun daga ranar da na shiga Musulunci har zuwa yau din nan, duk ranar Juma'a
sai na 'yanta bawa ko baiwa.
8. Tunda nake azamanin jahiliyya ko azamanin Musulunci ban ta'ba aikata zina
ba.
9. Tunda nake ban taba daukar kayan wani ba, ko azamanin jahiliyyah ko
azamanin Musulunci.
10. Na haddace Alqur'ani tun azamanin Manzon Allah (saww).
Jinjina agareka Ya Shugaban Muminai kuma Sarkinsu!! Ya
Uthmanu!! Wallahi Kaf acikin halittar Allah babu wanda ya tara wadannan darajojin
sai kai!!.
Yardodin Allah da amincinsa su tabbata agareka Ya Uthmanu tare da Manyan
abokananka guda 3, da dukkan Sahabban MAIGIDA (sallallahu alaihi wa alihi wa
sallam).

POPULAR POST

MAGANIN KARFIN MAZA KO MATA A MUSULUNCE

kala-kalar abincin dake samar da karfin maza/mata  (sperm), da kuma kuzari a jikin ango da amarya.
HATSI: 1. Alkama ko kuma duk wani dangin abinci da ake samarwa daga gareta. 2. Shinkafa. 3. Wake.

GANYE:
1. Albasa.
2. Galik.
3. Karas.
4. Dankali.
5. Kwakwa.

'YA' YAN ITATUWA:
1. Ayaba.
2. Mangoro.

DAREN FARKO (ABUNDA YA KAMATA SABBIN MA'AURATA SUYI A SHARI'ANCE)

1. Nafarko su fara da gaisuwa irin wadda addinin muslunci ya tanadar mana (watau suyi wa junan su sallama).

2. Sai ango ya daura hannunsa a bisa goshin amaryarsa ya karanta wannan addu'ar:

"Allahumma innee as'aluka min khairiha wa khairi maa jabaltaha 'alaihi wa'a uzhubika min sharriha wa sharri maa jabaltaha 'alaihi"
( Abu Dawud Ibn Maajah Al-Haakim Al-Bahaki da Abu ya'ala).

3. Daga nan sai ango da amarya su gabatar da Alwala sannan su gabatar da Sallah raka'a biyu bayan sun idar sai su karanta addu'o'i na neman 'ya'ya na gari.

FARILLAN ALWALA, SUNNONIN ALWALA, MUSTAHABBAN ALWALA DA KUMA YADDA AKE GYARA ALWALA

Farilla alwala: niyya da wanke fuska da wanke hannaye zuwa gwiwar hannu da shafar kai da wanke kafafuwa zuwa ido-sawu da cucudawa da gaggautawa.
Sunnonin alwala: wanke hannaye izuwa tsintsiyar hannu yayin farawa, da kurkure baki, da shaka ruwa, da fyacewa, da dawo da shafar kai, da shafar kunnuwa, da sabunta ruwa dan shafar kunnuwa, da jeranta farillai.

ISTIMNA'I (masturbation) da HUKUNCIN SA

ISTIMNA'I ( masturbation)

shine shine mutum ya rika wasa da al'aurassa har ya fitar da maniyyi,

HUKUNCIN ISTIMNA'I

Farko dai akwai hadisai wadanda suka nuna fushi na ubangiji akan mai aikata hakan,
Hukuncinsa ga malaman mazhabobi guda hudu,

Imam Malik Imam Shafi'i.
Sun tafi akan haramta shi don haka a wurin su dole mutum yayi aure ko ya kame har zuwa lokacin da Allah zai bashi ikon yin aure.

HUKUNCIN YIN JIMA'I DA AMARYA KO UWARGIDA TA DUBURA

Kamar yadda shari'a tayi hani akan aiwatar da jima'i ga uwargida ko amarya a lokacin da take haila, hakama jima'i ta dubura shari'a tayi hani mai tsanani akan aiwatar dashi.

MANZON ALLAH (S.A.W) yayi hani ga wadannan munanan aiyuka (jima'i a lokacin haila da jima'i ta dubura) a Hadisai da dama.

MANZON ALLAH  (S.A.W) yace: mutumin dake jima'i da matarsa ta dubura ALLAH Madaukakin Sarki ba zai dube shi da tausayi ba a ranar karshe.

Shehun malami Imam Ghazzali (R.A) ya rubuta a cikin littafinsa "IHYA" cewa yin jima'i da mace ta dubura yafi laifi mai tsanani akan yin jima'i da ita yayin da take haila. (A sani dukkansu laifukane masu tsanani)