Skip to main content

FASSARAR SALATUL FATIHI-DAGA MALAM JAMILU ABDULLAHI DUTSIN-MA

Allah kayi tsira ga sayyidina Annabi Mahammadu wanda ya bude abunda yake rufe ( Duniya ta kasance rufe da duhu manzon Allah yazo ya budeta da hasken musulunci) (Aljanna ta kasance rufe Annabi shine wanda zai budeta) ma'anar (الفاتح لما أغلق ) cikin sha'anin manzon yanada yawa na buga maka misali da 2.

(والخاتم لما سبق)
Wannan kuma ayar Qur'ani ce ta tabbatar masa da haka.
A cikin fadin Allah.
(ولكن رسول الله وخاتم النبيئين)
  Ma'ana Annabawa sun gabace shi shine cika makon annabawa.
ناصر الحق بالحق
Shi mai taimakon gaskiya ne tare da karfin gaskiyarsa ba don komai ba sai don tabbatar da gaskiya.
والهادي الي صراطك المستقيم.
Shima wannan ayar qur'ani ce ina Allah yake fadin ce

وإنك لتهدي الي صراط مستقيم
Hakika kai mai shiryatarwa ne ya zuwa tafarki madaidaici
وعلي ءاله
Kayi wannan tsira ya Allah ga Ahlinsa Saw.
حق قدره ومقداره العظيم
Dai dai gwargwadon darajarsa da girmansa a wurinka ya ubangiji

"Wadanda suka tafi akan cewa tafi duk wani salati farala sun dogara da wannan kalmar ta karshe domin kuwa shi kansa ya fadi cewa "
ﻻ يعرف حقيقتي اﻻ الله
Ma'ana babu wanda yasan ni ko waye sai Allahn da ya halicceni.

Allah ya kara mana soyayyarsa da kuma soyayyar masoyansa Amin. Nagode

Comments

POPULAR POST

MAGANIN KARFIN MAZA KO MATA A MUSULUNCE

kala-kalar abincin dake samar da karfin maza/mata  (sperm), da kuma kuzari a jikin ango da amarya.
HATSI: 1. Alkama ko kuma duk wani dangin abinci da ake samarwa daga gareta. 2. Shinkafa. 3. Wake.

GANYE:
1. Albasa.
2. Galik.
3. Karas.
4. Dankali.
5. Kwakwa.

'YA' YAN ITATUWA:
1. Ayaba.
2. Mangoro.

DAREN FARKO (ABUNDA YA KAMATA SABBIN MA'AURATA SUYI A SHARI'ANCE)

1. Nafarko su fara da gaisuwa irin wadda addinin muslunci ya tanadar mana (watau suyi wa junan su sallama).

2. Sai ango ya daura hannunsa a bisa goshin amaryarsa ya karanta wannan addu'ar:

"Allahumma innee as'aluka min khairiha wa khairi maa jabaltaha 'alaihi wa'a uzhubika min sharriha wa sharri maa jabaltaha 'alaihi"
( Abu Dawud Ibn Maajah Al-Haakim Al-Bahaki da Abu ya'ala).

3. Daga nan sai ango da amarya su gabatar da Alwala sannan su gabatar da Sallah raka'a biyu bayan sun idar sai su karanta addu'o'i na neman 'ya'ya na gari.

FARILLAN ALWALA, SUNNONIN ALWALA, MUSTAHABBAN ALWALA DA KUMA YADDA AKE GYARA ALWALA

Farilla alwala: niyya da wanke fuska da wanke hannaye zuwa gwiwar hannu da shafar kai da wanke kafafuwa zuwa ido-sawu da cucudawa da gaggautawa.
Sunnonin alwala: wanke hannaye izuwa tsintsiyar hannu yayin farawa, da kurkure baki, da shaka ruwa, da fyacewa, da dawo da shafar kai, da shafar kunnuwa, da sabunta ruwa dan shafar kunnuwa, da jeranta farillai.

ISTIMNA'I (masturbation) da HUKUNCIN SA

ISTIMNA'I ( masturbation)

shine shine mutum ya rika wasa da al'aurassa har ya fitar da maniyyi,

HUKUNCIN ISTIMNA'I

Farko dai akwai hadisai wadanda suka nuna fushi na ubangiji akan mai aikata hakan,
Hukuncinsa ga malaman mazhabobi guda hudu,

Imam Malik Imam Shafi'i.
Sun tafi akan haramta shi don haka a wurin su dole mutum yayi aure ko ya kame har zuwa lokacin da Allah zai bashi ikon yin aure.

HUKUNCIN YIN JIMA'I DA AMARYA KO UWARGIDA TA DUBURA

Kamar yadda shari'a tayi hani akan aiwatar da jima'i ga uwargida ko amarya a lokacin da take haila, hakama jima'i ta dubura shari'a tayi hani mai tsanani akan aiwatar dashi.

MANZON ALLAH (S.A.W) yayi hani ga wadannan munanan aiyuka (jima'i a lokacin haila da jima'i ta dubura) a Hadisai da dama.

MANZON ALLAH  (S.A.W) yace: mutumin dake jima'i da matarsa ta dubura ALLAH Madaukakin Sarki ba zai dube shi da tausayi ba a ranar karshe.

Shehun malami Imam Ghazzali (R.A) ya rubuta a cikin littafinsa "IHYA" cewa yin jima'i da mace ta dubura yafi laifi mai tsanani akan yin jima'i da ita yayin da take haila. (A sani dukkansu laifukane masu tsanani)