Skip to main content

Posts

Showing posts from September, 2014

FASSARAR SALATUL FATIHI-DAGA MALAM JAMILU ABDULLAHI DUTSIN-MA

Allah kayi tsira ga sayyidina Annabi Mahammadu wanda ya bude abunda yake rufe ( Duniya ta kasance rufe da duhu manzon Allah yazo ya budeta da hasken musulunci) (Aljanna ta kasance rufe Annabi shine wanda zai budeta) ma'anar (الفاتح لما أغلق ) cikin sha'anin manzon yanada yawa na buga maka misali da 2. (والخاتم لما سبق) Wannan kuma ayar Qur'ani ce ta tabbatar masa da haka. A cikin fadin Allah. (ولكن رسول الله وخاتم النبيئين)   Ma'ana Annabawa sun gabace shi shine cika makon annabawa. ناصر الحق بالحق Shi mai taimakon gaskiya ne tare da karfin gaskiyarsa ba don komai ba sai don tabbatar da gaskiya. والهادي الي صراطك المستقيم. Shima wannan ayar qur'ani ce ina Allah yake fadin ce وإنك لتهدي الي صراط مستقيم Hakika kai mai shiryatarwa ne ya zuwa tafarki madaidaici وعلي ءاله Kayi wannan tsira ya Allah ga Ahlinsa Saw. حق قدره ومقداره العظيم Dai dai gwargwadon darajarsa da girmansa a wurinka ya ubangiji "Wadanda suka tafi akan cewa tafi duk wani salati