Skip to main content

KADAN DAGA YADDA BILAL YAKE SON SHUGABA S.A.W

WANI LAMARI MAI GIRGIZA ZUCCIYAR MASOYAN ANNABI MUHAMMADU S.A.W YA
FARU BAYAN WAFATINSA
yayinda sayyiduna Bilal yaga damuwa da kadaicin rabuwa da babban masoyinmu ya tsananta gareshi madina ta zamemashi tamkar keji abu ya zamo ko kiransallah
baya iyayi domin da ya kawo wurin "ASH HADU ANNA MUHAMMADURRASULULLAH" sai
yaji muryarsa ta shake ta tsaya don kuka da kaunar annabi S.A.W gani yake kamar zai waiwaya yagansa .
Da yaga abu yatsananta gareshi saiya nemi iznin khalifa sayyiduna Abubakar Assaddiq R.A don ya tashi ya koma kasar Sham ya zauna acan tareda wasu cikin
sahabban manzon Allah. 


Ya nacan zaune tsawon lokaci sai rannan kwatsam yayi mafarki da shugaban halittun Allah Annabi Muhammadu S.A.W yana ce masa :

YAKAI BILAL WANNAN WACE IRIN KEKASHEWACE ? HAR YANZU LOKACI BAI ZOBA DA
ZAKAZO KA ZIYARCEMUBA ?

Ko da sayyiduna Bilal ya farka bai jira komaiba ya hau doki a guje bai zame koinaba sai Madina yana zuwa yazarce dausayin aljanna a duniya Rauda ma daukakiya makwantar annabin farko da karshe annabin rahama S.A.W ya isa gaban fiyayyen kabari yana kuka yana birgima yana dibar kasa yana zuba ma kansa . 
Ana cikin haka jikokin annabin tsira sadatuna Hassan da Hussaini R.A suka tarar dashi suka rinka goge masa kasa suma suna kuka suna rungume dashi.
Daganan aka nemi alfarmar yayi kiran sallah, baiyi gardamaba ya hau mumbari ya fara kira saiga masallaci ya cika da jamaa daga ko ina ana kyarma ana tunanin Annabi Muhammadu s.a.w dai dai lokacin da ya ambaci 

"ASH HADU ANNA MUHAMMADURRASULULLAH " 

Gaba daya kowa dake wurin saida ya barke da kukan tunawa da annabi Muhammadu S.A.W .

ALLAH KABAMU ALBARKACIN MASOYAN ANNABI MUHAMMADU S.A.W DUK INDA SUKE
KA AZURTAMU DA WANNAN SOYAYYA A ZAHIRI DA BADININMU

Salati 10 ga Annabi S.A.W 

Comments

POPULAR POST

MAGANIN KARFIN MAZA KO MATA A MUSULUNCE

kala-kalar abincin dake samar da karfin maza/mata  (sperm), da kuma kuzari a jikin ango da amarya.
HATSI: 1. Alkama ko kuma duk wani dangin abinci da ake samarwa daga gareta. 2. Shinkafa. 3. Wake.

GANYE:
1. Albasa.
2. Galik.
3. Karas.
4. Dankali.
5. Kwakwa.

'YA' YAN ITATUWA:
1. Ayaba.
2. Mangoro.

DAREN FARKO (ABUNDA YA KAMATA SABBIN MA'AURATA SUYI A SHARI'ANCE)

1. Nafarko su fara da gaisuwa irin wadda addinin muslunci ya tanadar mana (watau suyi wa junan su sallama).

2. Sai ango ya daura hannunsa a bisa goshin amaryarsa ya karanta wannan addu'ar:

"Allahumma innee as'aluka min khairiha wa khairi maa jabaltaha 'alaihi wa'a uzhubika min sharriha wa sharri maa jabaltaha 'alaihi"
( Abu Dawud Ibn Maajah Al-Haakim Al-Bahaki da Abu ya'ala).

3. Daga nan sai ango da amarya su gabatar da Alwala sannan su gabatar da Sallah raka'a biyu bayan sun idar sai su karanta addu'o'i na neman 'ya'ya na gari.

FARILLAN ALWALA, SUNNONIN ALWALA, MUSTAHABBAN ALWALA DA KUMA YADDA AKE GYARA ALWALA

Farilla alwala: niyya da wanke fuska da wanke hannaye zuwa gwiwar hannu da shafar kai da wanke kafafuwa zuwa ido-sawu da cucudawa da gaggautawa.
Sunnonin alwala: wanke hannaye izuwa tsintsiyar hannu yayin farawa, da kurkure baki, da shaka ruwa, da fyacewa, da dawo da shafar kai, da shafar kunnuwa, da sabunta ruwa dan shafar kunnuwa, da jeranta farillai.

ISTIMNA'I (masturbation) da HUKUNCIN SA

ISTIMNA'I ( masturbation)

shine shine mutum ya rika wasa da al'aurassa har ya fitar da maniyyi,

HUKUNCIN ISTIMNA'I

Farko dai akwai hadisai wadanda suka nuna fushi na ubangiji akan mai aikata hakan,
Hukuncinsa ga malaman mazhabobi guda hudu,

Imam Malik Imam Shafi'i.
Sun tafi akan haramta shi don haka a wurin su dole mutum yayi aure ko ya kame har zuwa lokacin da Allah zai bashi ikon yin aure.

HUKUNCIN YIN JIMA'I DA AMARYA KO UWARGIDA TA DUBURA

Kamar yadda shari'a tayi hani akan aiwatar da jima'i ga uwargida ko amarya a lokacin da take haila, hakama jima'i ta dubura shari'a tayi hani mai tsanani akan aiwatar dashi.

MANZON ALLAH (S.A.W) yayi hani ga wadannan munanan aiyuka (jima'i a lokacin haila da jima'i ta dubura) a Hadisai da dama.

MANZON ALLAH  (S.A.W) yace: mutumin dake jima'i da matarsa ta dubura ALLAH Madaukakin Sarki ba zai dube shi da tausayi ba a ranar karshe.

Shehun malami Imam Ghazzali (R.A) ya rubuta a cikin littafinsa "IHYA" cewa yin jima'i da mace ta dubura yafi laifi mai tsanani akan yin jima'i da ita yayin da take haila. (A sani dukkansu laifukane masu tsanani)