Skip to main content

HADISI MAI BAN TSORO

Wannan kuwa shine Hadisin da Bukhari Da Muslim suka ruwaito cewa:

 Manzon Allah S.A.W. Ya ce: "Mai ZINA ba ya yin ZINA a lokacin da yake yin ZINA A halin
yana da IMANI, haka nan BARAWO ba yin sata a lokacin da yake SATA a halin yana Mumini, Haka kuma Mashayin GIYA ba zai sha GIYA ba a lokacin da yake shan GIYA a halin yana Mumini. Kuma mai kwace ba zai kwace kayan wani ba, kayan da Mutane za su daga ido su Kyale shi saboda mamakin taurin zuciyarsa a halin yana matsayin Mumini, Haka nan mai Satar ganima ba zai sace ganima ba a halin yana matsayin Mumini.
Saboda haka ku yi hankali da kanku ku yi hankali da Kanku.
Haka ya zo a cikin Littafin Almishkat' a Babin Alkaba'ir.


Ya Dan'UwaNa/ 'Yar'UwaTa a cikin Soyayyar Allah Da Manzon Sa S.A.W. Wadannan ayyukan da aka ambata a cikin Hadisin Bukhari da Muslim suka ruwaito shi, Ko da yake dai kanana ne a idon ka/ki, Kuma sai dai a bar su saboda tsoron Allah kuma domin fifita lahirarka a kan duniyarka lallai Allah Zai gafarta maka, saboda la'akari da fadin Allah
Madaukakin Sarki
"AMMA KUMA DUK WANDA YA JI TSORON TSAYAWA A GABAN UBANGIJISA, KUMA YA HANA ZUCIYARSA TA AIKATA ABIN DA TAKE SO TO LALLAI ALJANNA ITA CE MAKOMA {A WAJENSA}." Surah Nazi'at 40-41.
Wannan kuwa ba ya sabawa da cewa, duk wanda ya yi shishshigi kuma ya saba wa Umarnin Allah ya fifita rayuwar duniya a kan ta lahira sannan bai hana zuciyarsa aikata abin da take so ba, to wannan makomarsa ita ce "JAHANNAMA". Saboda aikata wannan mummunan aiki. Lallai Allah Ya yi Gaskiya da Yakecewa: 

"DUK WANDA YA YI SHISHSHIGI KUMA YA FIFITA RAYUWAR DUNIYA A KAN TA LAHIRA TO LALLAI WUTAR JAHANNAMA ITA CE MAKOMA". Surah Nazi'ar 38-39.

Allah Ya Kiyaye Mu Daga Wannan Abu. Ameen

Salati 10 ga Annabi S.A.W 

Comments

POPULAR POST

MAGANIN KARFIN MAZA KO MATA A MUSULUNCE

kala-kalar abincin dake samar da karfin maza/mata  (sperm), da kuma kuzari a jikin ango da amarya.
HATSI: 1. Alkama ko kuma duk wani dangin abinci da ake samarwa daga gareta. 2. Shinkafa. 3. Wake.

GANYE:
1. Albasa.
2. Galik.
3. Karas.
4. Dankali.
5. Kwakwa.

'YA' YAN ITATUWA:
1. Ayaba.
2. Mangoro.

DAREN FARKO (ABUNDA YA KAMATA SABBIN MA'AURATA SUYI A SHARI'ANCE)

1. Nafarko su fara da gaisuwa irin wadda addinin muslunci ya tanadar mana (watau suyi wa junan su sallama).

2. Sai ango ya daura hannunsa a bisa goshin amaryarsa ya karanta wannan addu'ar:

"Allahumma innee as'aluka min khairiha wa khairi maa jabaltaha 'alaihi wa'a uzhubika min sharriha wa sharri maa jabaltaha 'alaihi"
( Abu Dawud Ibn Maajah Al-Haakim Al-Bahaki da Abu ya'ala).

3. Daga nan sai ango da amarya su gabatar da Alwala sannan su gabatar da Sallah raka'a biyu bayan sun idar sai su karanta addu'o'i na neman 'ya'ya na gari.

FARILLAN ALWALA, SUNNONIN ALWALA, MUSTAHABBAN ALWALA DA KUMA YADDA AKE GYARA ALWALA

Farilla alwala: niyya da wanke fuska da wanke hannaye zuwa gwiwar hannu da shafar kai da wanke kafafuwa zuwa ido-sawu da cucudawa da gaggautawa.
Sunnonin alwala: wanke hannaye izuwa tsintsiyar hannu yayin farawa, da kurkure baki, da shaka ruwa, da fyacewa, da dawo da shafar kai, da shafar kunnuwa, da sabunta ruwa dan shafar kunnuwa, da jeranta farillai.

ISTIMNA'I (masturbation) da HUKUNCIN SA

ISTIMNA'I ( masturbation)

shine shine mutum ya rika wasa da al'aurassa har ya fitar da maniyyi,

HUKUNCIN ISTIMNA'I

Farko dai akwai hadisai wadanda suka nuna fushi na ubangiji akan mai aikata hakan,
Hukuncinsa ga malaman mazhabobi guda hudu,

Imam Malik Imam Shafi'i.
Sun tafi akan haramta shi don haka a wurin su dole mutum yayi aure ko ya kame har zuwa lokacin da Allah zai bashi ikon yin aure.

HUKUNCIN YIN JIMA'I DA AMARYA KO UWARGIDA TA DUBURA

Kamar yadda shari'a tayi hani akan aiwatar da jima'i ga uwargida ko amarya a lokacin da take haila, hakama jima'i ta dubura shari'a tayi hani mai tsanani akan aiwatar dashi.

MANZON ALLAH (S.A.W) yayi hani ga wadannan munanan aiyuka (jima'i a lokacin haila da jima'i ta dubura) a Hadisai da dama.

MANZON ALLAH  (S.A.W) yace: mutumin dake jima'i da matarsa ta dubura ALLAH Madaukakin Sarki ba zai dube shi da tausayi ba a ranar karshe.

Shehun malami Imam Ghazzali (R.A) ya rubuta a cikin littafinsa "IHYA" cewa yin jima'i da mace ta dubura yafi laifi mai tsanani akan yin jima'i da ita yayin da take haila. (A sani dukkansu laifukane masu tsanani)